‘Yadda Yahaya Bello Ya Yaudare Ni Kwana 1 kafin Zaben Fidda Gwani’: Mataimakinsa

‘Yadda Yahaya Bello Ya Yaudare Ni Kwana 1 kafin Zaben Fidda Gwani’: Mataimakinsa

  • Tsohon mataimakin gwamnan Jihar Kogi, Edward Onoja, ya ce Yahaya Bello ya dade yana shaida masa zai gaje shi kafin sauya ra’ayi
  • Onoja ya bayyana cewa Bello ya umurce su su sayi fom na APC, amma daga bisani ya goyi bayan Ahmed Usman Ododo a matsayin magaji
  • Duk da rasawa, Onoja ya ce ya cigaba da kasancewa tare da APC, ya kuma yi aiki domin nasarar Ododo a zaben 2023

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lokoja, Kogi - Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kogi, Edward Onoja, ya tuna yadda ta kaya tsakaninsa da Yahaya Bello a jihar.

Onoja ya bayyana cewa tsohon gwamnan da kansa ya shaida masa tsawon shekaru hudu cewa zai gaje shi.

Mataimakin Yahaya Bello ya fadi yadda suka yi kan kujerar gwamna a Kogi
Tsohon gwamna Yahaya Bello da mataimakinsa, Edward Onoja. Hoto: Alhaji Yahaya Bello.
Source: Facebook

Mataimakin Yahaya Bello ya yi tone-tone

Onoja, wanda yanzu yake mamba a hukumar Ci gaba yankin Kudu maso Kudu, ya yi wannan bayani a tattaunawa da aka watsa a MIC ON Podcast da Punch ta bibiya.

Kara karanta wannan

"Ka daina kawo rudani": An shawarci Wike ya zaba tsakanin APC ko PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya tuna cewa kafin zama mataimaki, ya fara matsayin shugaban ma'aikata inda Bello ya shaida masa koyaushe ya shirya domin ya gaje shi a nan gaba.

“Tsawon shekaru hudu kafin 2023, shi (Yahaya Bello) ne ya kira ni ya ce, ‘Kai zaka gaje ni, ka shirya.’ Kuma na yi shiri.
"Na yi aiki, lokacin da aka kai ga zabe, ya ba mu dama mutum bakwai da mu shiga takara.”

Umarnin da Yahaya Bello ya ba su kan takara

Onoja ya kara bayyana cewa Bello ya umurci kimanin mambobin majalisa bakwai, ciki har da shi, da su saya fom din APC na neman takara.

Sai dai daga baya Bello ya sauya ra’ayi, ya koma goyon bayan gwamna na yanzu, Ahmed Usman Ododo, a matsayin zabinsa na gaskiya.

“A karshe zuciyarsa da zabinsa sun kasance tare da gwamna na yanzu, Mai girma, Alhaji Ahmed Usman Ododo."

Kara karanta wannan

Rigima ta barke tsakanin Ministan Tinubu da gwamna a APC? An samu bayanai

Yahaya Bello ya manta mataimakinsa bayan masa alkawarin gadon kujerarsa
Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello yayin da yake mulkin jihar. Hoto: Alhaji Yahaya Bello.
Source: Facebook

Martanin Onoja bayan Yahaya Bello ya fada masa

Onoja ya bayyana cewa Bello ya sanar da shi wannan sauyin ra’ayi kwana daya kafin zaben fidda gwani, abin da ya karba cikin natsuwa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

“Lokacin da ya sanar da ni kwana daya kafin zaben, na ce masa, ‘Kai ne oga, abin da ka gani shi nake gani.’”

- Cewar Onoja

Onoja ya ci gaba da cewa, duk da jin takaici, ya zauna a jam’iyyar APC, inda ya yi aiki domin nasarar Gwamna Usman Ododo a zaben Nuwamba 2023.

Ya jaddada cewa ya kasance mai biyayya ga jam’iyyar da tsohon gwamna, yana tabbatar da kyakkyawan aiki domin ci gaban tafiyar siyasar APC.

Yahaya Bello ya umarci yan majalisa kan Ododo

Mun ba ku labarin cewa an yaɗa wani faifan bidiyo da aka gano tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, yana ba yan majalisar dokokin jiharsa umarni.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya gaji da zama haka, zai nemi takarar gwamna karkashin APC

Yahaya Bello ya bukaci 'yan majalisar dokoki su mara wa Gwamna Usman Ododo baya, domin ci gaban jihar gaba ɗaya.

A bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta, Bello ya umarci manyan mutanen su zauna ƙasa, hakan ya jawo sukar jama'a.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.