'Abin da Goodluck Jonathan da Peter Obi suka Tattauna yayin Ganawarsu'
- Wasu na kallon ganawar Peter Obi da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a matsayin wani shiri na siyasa gabanin 2027
- Hadimin Peter Obi ya fito ya yi magana kan abin da ya sanya manyan mutanen guda biyu suka gana cikin tsakiyar makon nan
- Peter Obi dai yana ci gaba da ganawa da manyan ’yan siyasa a fadin kasar nan yayin da ake tunkarar babban zabe na 2027
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja – Jagoran kungiyar Obidient Movement, Yunusa Tanko, ya yi magana kan ganawar da Peter Obi ya yi da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Yunusa Tanko ya karyata rade-radin da ke cewa Peter Obi, ya gana da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ne domin neman goyon baya kan zaben 2027

Source: Twitter
Hadimin na Peter Obi ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da jaridar The Punch.

Kara karanta wannan
Bayan ganin sun hadu da Peter Obi, magoya baya sun aikawa Jonathan bukatarsu a 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ba siyasa a ganawar Jonathan da Peter Obi
Yunusa Tanko ya bayyana cewa ganawar da Peter Obi ya yi da Jonathan kwanan nan a Abuja ba ta da alaka da siyasa, illa tattaunawa kan halin da kasar nan ke ciki.
“Akwai dadaddiyar alaka tsakanin Obi da Jonathan. Don haka ba ta da nasaba da siyasa ko neman goyon baya. Maganar kasa ake yi."
- Yunusa Tanko
Tattaunawar dai wadda Peter Obi ya bayyana a matsayin mai muhimmanci, ta jawo cece-kuce cewa akwai yiwuwar yin hadaka tsakaninsu kan siyasa gabanin 2027.
Sai dai, Yunusa Tanko ya dage cewa babu wata manufa ta siyasa a cikin wannan haduwarr da manyan mutanen guda biyu suka yi.
"Jonathan da Peter Obi sun sha ganawa ba tare da sanin jama'a ba. A takaice mutane ba su fara ba hakan muhimmanci ba har sai da aka fara maganganun Jonathan zai yi takara."
"Sun dade suna aiki tare. Don haka ka da a dauka yaje neman goyon bayansa ne. Jonathan dattijo ne a siyasa, Peter Obi ma yana tunkarar wannan matsayi. Kasar nan na dab da rugujewa, abin da ya kamata mu damu a kai shi ne yadda za mu ceto ta."
- Yunusa Tanko

Source: Facebook
Peter Obi na ganawa da 'yan siyasa
Peter Obi, wanda ya zama na uku a zaben shugaban kasa na shekarar 2023, ya ci gaba da tattaunawa da manyan ’yan siyasa a fadin kasar nan, abin da wasu ke gani a matsayin shirin kara bunkasa siyasarsa.
Tun bayan barin mulki a shekarar 2015, Goodluck Jonathan ya rungumi matsayin dattijo a nahiyar Afrika, yana shiga tsakani a rikice-rikicen siyasa tare da kare dimokuradiyya.
Jam'iyyar LP ta kalubalanci Peter Obi
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar LP ta bayyana cewa za ta raba gari da dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi.
Sakataren yada labarai na kasa na LP, Abayomi Ararambi, ya bayyana cewa ba za su ba Peter Obi, tikitin yin takarar shugaban kasa a 2027 ba.
Hakazalika, Abayomi Ararambi ya kalubalanci tsohon dan takarar shugaban kasan kan ya fito fili ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
