Bayan Ganin Sun Hadu da Peter Obi, Magoya Baya Sun Aikawa Jonathan Bukatarsu a 2027

Bayan Ganin Sun Hadu da Peter Obi, Magoya Baya Sun Aikawa Jonathan Bukatarsu a 2027

  • 'Yan kungiyar Obidients, magoya bayan tsohon dan takarar Shugaban Kasa, Peter Obi sun hango haske a zaben 2027 da ke tafe
  • Bayan sun ga jagoransu da tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Ebele Jonathan, sun bayyana cewa akwai bukatar sadaukar da kai
  • Bukatarsu na zuwa bayan Obi da Jonathan sun gana a bayan fage sau uku tsakanin watan Disamban bara zuwa yanzu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Magoya bayan Peter Obi baya karkashin kungiyar Obidient Movement sun bayyana bukatarsu ga tsohon shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan.

Bayan sun ga tsohon Shugaban da tsohon dan takarar Shugaban kasa a LP, 'yan Obidents sun nemi Goodluck Jonathan ya hakura da batun takara a 2027.

Kara karanta wannan

Shirin kifar da Tinubu: Peter Obi ya gana da Goodluck Jonathan a Abuja

Obi ya gana da Jonathan
Hoton Peter Obi da Goodluck Jonathan Hoto: Peter Obi
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa wannan kiran ya zo ne bayan wata ganawar sirri da aka yi tsakanin Obi da Jonathan a birnin Abuja ranar Alhamis.

2027: Peter Obi da Goodluck Jonathan sun gana

Tattaunawar ranar Alhamis tsakanin Peter Obi da Goodluck Jonathan ta kara rura yiwuwar sabuwar hadakar ‘yan adawa gabanin zaben 2027.

Ko da yake ba a bayyana cikakken abin da suka tattauna ba, Peter Obi ya wallafa hotunan ganawar a shafinsa na X, inda ya bayyana Jonathan a matsayin babban yaya, dattijo kuma jagoran kasa.

Sai dai shugaban riko na Obidient Movement, Dr. Yunusa Tanko, ya ce a duk da Obi da Jonathan dukkanninsu manyan mutane ne masu kima, amma Obi ne zabin miliyoyin ‘yan Najeriya.

Mabiya Obi na son Jonathan ya kauce masu a zaben 2027
Hoton Peter Obi yana wata gana wa da manema labarai Hoto: Peter Obi
Source: Twitter

Ya ce:

“Jonathan ya taka rawar gani a matsayin shugaban kasa, lokaci ya yi da zai tallafa wa dan uwansa domin a ceto Najeriya. Obi ya tsaya tare da shi lokacin yana mulki, yanzu lokaci ne na rama wa kura aniyarta."

Kara karanta wannan

Tinubu da kansa ya fadi abubuwan da ya tattauna da shugaban Kasar Faransa

Ana maganganu a kan Obi da Jonathan

Dr. Tanko ya kara da cewa akwai wasu ‘yan siyasa da ke kokarin amfani da Jonathan a matsayin makami don rage karfin Obi a zaben 2027, amma Obidient ta ce ba haka ba ne.

Ya ce:

“Mun san akwai wasu dabaru da ake kokarin cusa wa, amma mun yi imani ba za su yi nasara ba."

Yayin da PDP da wasu daga cikin ADC ke lallaba Jonathan saboda suna ganin yana da karbuwa a Arewacin kasar, mabiya Obi na ganin cewa karfin Obidient zai fi tasiri.

Yadda Obi ya gana da Jonathan a Abuja

A wani labarin, mun wallafa cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, ya yi ganawar sirri da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a Abuja ranar Alhamis.

Rahotanni sun tabbayar da cewa ganawar ta mayar da hankali ne kan tarin ƙalubale da Najeriya ke fuskanta, da yadda za a iya samo mafita, musamman ta fuskar siyasa.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro da ƴan bindiga sun gwabza ƙazamin faɗa a Malumfashi, an rasa rayuka

Duk da haka, ba a bayyana karara abin da suka tattauna ba, amma lokaci da yanayin ganawar sun jawo ce‑ce‑ku‑ce sosai a tsakanin al’umma ganin cewa 2027 na karato wa a nan kusa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng