Natasha: NLC Ta Fara Shirin Hada Gangamin Zanga Zanga kan Hana Sanata Koma wa Majalisa

Natasha: NLC Ta Fara Shirin Hada Gangamin Zanga Zanga kan Hana Sanata Koma wa Majalisa

  • NLC ta yi barazanar tura mambobinta gaban Majalisar Tarayya idan ba a bar Sanata Natasha ta koma bakin aiki ba
  • Kungiyar 'yan kwadagon ta kasa ta zargi majalisar dattawa da take dokar kasa da kuma tauye dimokuradiyya
  • Shugaban NLC, Joe Ajaero ya ce hana Natasha dawowa bayan karewar dakatarwarta ya sabawa hukuncin kotu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC), Joe Ajaero, ya kalubalanci Majalisar Dattawa karkashin Sanata Godswill Akpabio.

Ya ce majalisa ta karya doka saboda hana Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta Kogi ta Tsakiya dawowa bakin aikinta duk da karewar lokacin dakatarwarta.

NLC ta fusata kan hana Natasha koma wa aiki
Hoton Sanata Natasha da wani bangare na zauren majalisar dattawa Hoto: Natasha H Akpoti/The Nigerian Senate
Source: Facebook

Premium Times ta wallafa cewa Ajaero ya bayyana cewa wannan mataki ya sabawa dimokuradiyyar da 'yan kasar nan ke tafiya a kai.

Kara karanta wannan

Murna ta koma ciki? Gwamnatin tarayya ta karyata shirin daukar sababbin ma'aikata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC ta fusata kan hana Sanata Natasha aiki

Tribune Online ta wallafa cewa Shugaban NLC, Joe Ajaero ya bayyana cewa hana Sanata Natasha koma wa aiki wata barazana ce ga dokar kasa da hakkokin masu jefa kuri’a.

Ya ce:

"Wannan ba kuskure ba ne kawai, karan tsaye ce ga dimokuradiyya. Abin da ake yi wa Sanata yau, hari ne ga hakkin masu jefa kuri’a gobe."

Kungiyar kwadagon ta NLC ta gargadi Majalisar Tarayya cewa za ta iya fito da dimbin 'ya'yanta domin nuna adawa da ci gaba da hana Sanata Natasha komawa kujerart.

Kungiyar ta nanata cewa wannan mataki da majalisar ke kai ya nuna tsantsar rashin adalci ne da cin zarafin dokar kasa.

Kungiyar NLC ta zargi majalisa da danniya

A cikin sanarwar, Joe Ajaero ya zargi majalisar dattawa da kokarin amfani da shari’a don murkushe ‘yan adawa da kuma hana su fadin ra’ayoyinsu.

Kara karanta wannan

Najeriya na fuskantar matsin lamba daga ƙetare, ana so Natasha ta koma majalisa

Ya bayyana cewa dalilin cewa shari’ar tana gaban kotu bayan karewar dakatarwar wata shida da aka ayyana a baya, ba hujja ce da za a iya jingina da ita ba.

NLC ta fara shirin zanga-zanga
Hoton Natasha, dakatacciyar Sanata mai WAKILTAR kOGI TA Tsakiya Hoto: Natsha H Akpoti
Source: Facebook

Ya ce:

"Kare dakatarwa da kotu ta soke, babban rashin kunya ne da take doka. Wannan ba tsarin dimokuradiyya bane."

Haka kuma, Ajaero ya ce hana Sanata Natasha ta koma aiki babban cin fuska ne ga mutanen Kogi ta Tsakiya da suka zabe ta, tare da cire masu wakilcin da ya dace su samu a majalisar dattawa.

Ya kara da cewa kungiyar NLC tana kallon wannan lamari a matsayin yunkuri na wasu ‘yan siyasa masu hannu da shuni wajen dorawa al’umma mulki na danniya da rashin adalci.

Majalisa ta hana Natasha koma wa aiki

A wani labarin, mun wallafa cewa Majalisar Dattawan Najeriya ta bayyana cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ba za ta iya komawa kujerarta ba.

Majalisar ta sanar da hakan ne ta wata wasika da mukaddashin Magatakardar Majalisar, Dr. Yahaya Danzaria, ya aikawa Sanata Natasha bayan cikar wa'adin dakatarwarta.

Sai dai majalisar ta ce babu wani izini ko cikakken hukunci daga kotu da ya ba ta damar dawowa, don haka ba za a amince da dawowarta ba a halin yanzu har sai abin da hali ya yi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng