2027: Malaman Musulunci Sun Yi Ruwan Addu’o’i ga Tinubu da Barau a Kano, an Yi Yanka

2027: Malaman Musulunci Sun Yi Ruwan Addu’o’i ga Tinubu da Barau a Kano, an Yi Yanka

  • Wata kungiya a jihar Kano ta shirya addu’o’i na musamman domin samun nasarar shugaban kasa, Bola Tinubu da Sanata Barau Jibrin
  • Kungiyar ta kunshi malaman Musulunci inda suka yi karatun Alkur'ani mai girma saboda samun nasara a zaben 2027 mai zuwa
  • Malaman sun yi addu'o'i ga Tinubu da Barau, suna roƙon zaman lafiya, cigaban tattalin arziki, da kwanciyar hankali a ƙasar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Gabanin zaben 2027, wata kungiya a jihar Kano ta gudanar da addu'o'oi na musamman kan yan siyasar a jihar karkashin APC.

Kungiyar mai suna 'Tinubu/Barau/Atah Movement' ta shirya addu’a a Kano domin samun nasarar Shugaba Bola Tinubu da Sanata Barau Jibrin.

Tinubu da Barau sun sha ruwan addu'o'i a Kano
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Barau I Jibrin, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

An yi addu'o'in samun nasarar Tinubu da Barau

An gudanar da addu’ar ne a Gidan Baballiya Kurna, inda malamai da magoya bayan APC daga ƙananan hukumomi 44 suka halarta, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda a Katsina, an tura miyagu zuwa barzahu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malaman sun kammala karatun Alkur’ani tare da addu’o’i na musamman domin Tinubu ya samu wa’adi na biyu da burin gwamna na Barau.

Sun yi addu’a ga zaman lafiya mai dorewa, cigaban tattalin arziki da cigaban ƙasa, da tabbatar da kwanciyar hankali a Najeriya baki ɗaya.

Daya daga cikin wadanda suka shirya addu'o'in, Seyi Olorunshaya ya ce an shirya taron domin tallafa wa sake zaɓen Tinubu da burin Barau na zama gwamnan Kano a 2027.

Ya ce:

“Shugaba Tinubu ya yi abubuwa da dama cikin shekaru biyu, aikin hanyoyi, saukar farashin kayan abinci, da ƙoƙarin kawo tsaro.”
An yi addu'o'i ga Barau da Tinubu kan zaben 2027
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin. Hoto: Barau I Jibrin.
Source: Facebook

Abin da ake tsammani idan Barau ya zarce

Olorunshaya ya ƙara da cewa abubuwan da suka daɗe suna damun jama’a kamar tsaro da tsadar rayuwa suna samun gyara cikin ‘yan shekarun nan.

Ya kara da cewa:

“Muna da abin da za mu gabatar da shugabamu domin wa’adi na biyu. Jama’a za su ga al’ajabi idan aka sake zaɓarsa.”

Kara karanta wannan

Boko Haram: Tinubu ya ba da umarnin gaggawa bayan kisan mutum 63 a Borno

Olorunshaya ya bayyana cewa Barau shi ne mutum mafi ƙarfi da zai iya karɓe iko daga hannun NNPP a Kano a babban zabe mai zuwa.

Jagoran malaman, Saminu Khalid Abdullahi, ya ce:

“TBA sabuwar ƙungiya ce da aka kafa don tallafa wa Tinubu, Barau da Atah.”

Saminu ya ƙara da cewa burin ƙungiyar shi ne haɗa jama’a don tallafawa gwamnati da ƙarfafa zumunci gabanin zaben 2027 mai zuwa.

Bayan addu’ar, aka yanka rago a matsayin hadaya don neman nasara ga Tinubu da Barau a zaben mai zuwa.

A Kano, magoya baya na tallata Barau a matsayin ɗan takarar APC mafi ƙarfi da zai iya fuskantar NNPP a 2027.

Malaman Tijjaniya sun gana da Tinubu

Kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi sallar Juma'a tare da malaman Ɗarikar Tijjaniyya a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Manyan malaman karkashin Khalifa Mahiy Sheikh Ibrahim Nyass sun tattauna da Tinubu tare da yin addu'o'i bayan kammala sallah.

Shugabannin Tijjaniyar sun yaba wa shugaban ƙasa bisa karimci da kulawar da yake nuna masu tare da fatan samun zaman lafiya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.