2027: APC Ta ba 'Yan Adawa Satar Amsa, Ta Fadi Kuskuren Atiku, Obi da El Rufa'i
- Jam’iyyar APC ta karyata zargin Aminu Waziri Tambuwal da ya ce gwamnati mai ci na shirin rusa jam’iyyun adawa a Najeriya
- Mai magana da yawun APC, Felix Morka, ya ce Tambuwal da sauran shugabannin adawa ne suka gaza samar da tsari a tafiyarsu
- APC ta danganta binciken da hukumar EFCC ke yi game da Aminu Tambuwal kan zargin almundahana da cewa ba siyasa ba ne
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta maida martani ga tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, kan zargin da ya yi cewa gwamnati mai ci da APC na shirin rusa 'yan adawa.
A cewar APC, kalaman Tambuwal ba su da tushe, domin a zahiri shi da sauran shugabannin jam’iyyun adawa ne suka gaza samar da shugabanci mai nagarta ga magoya bayansu.

Source: Facebook
Tashar NTA ta wallafa a X cewa mai magana da yawun jam’iyyar, Felix Morka ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Morka ya kalubalanci Tambuwal kan zarge-zargen da ya yi a wani shiri na talabijin a makon da ya gabata.
Zargin Tambuwal kan APC gabanin 2027
A cikin hirarsa da tashar Channels Television, Tambuwal ya yi zargin cewa Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC na shirye-shiryen raunana jam’iyyun adawa kamar PDP da LP.
Ya ce alamomin wannan shiri sun bayyana sosai, yana mai jaddada cewa ba wai zato kawai yake yi ba, domin a cewarsa akwai shaidu masu gamsarwa.
Haka kuma, Tambuwal ya bayyana cewa kokarin kawar da Tinubu a 2027 ba na Arewa kawai ba ne, illa kawai wani yunkuri ne da ya kunshi al’umma daga sassa daban-daban na ƙasa.
APC ta daurawa Atiku da Peter Obi laifi
Da yake mayar da martani, Felix Morka ya ce zargin Tambuwal ba shi da hujja, yana mai cewa akasin haka shi da sauran manyan ’yan adawa ne suka jefa jam’iyyunsu cikin rudani.
Ya bayyana cewa fitattun ’yan adawa irin su Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai, Peter Obi da Rotimi Amaechi duk sun gaza wajen samar da shugabanci nagari ga jam’iyyunsu.
A cewarsa, abin mamaki ne ganin yadda wadannan mutane da suka taba rike manyan mukamai amma suka kasa samar da tsari, shugabancin da zai bunkasa jam’iyyunsu.

Source: Facebook
Tambuwal: Batun EFCC da siyasa
Sanarwar ta kuma tabo binciken da hukumar EFCC ke yi wa Tambuwal kan zargin cire kudi har Naira biliyan 189 da ya saba wa dokar hana almundahana ta shekarar 2022.
Morka ya ce ba siyasa a tattare da binciken, illa kawai wani yunkuri ne na Tambuwal domin gujewa hukunci.
Premium Times ta rahoto ya kara da cewa:
“Dole Tambuwal ya fahimci cewa kasancewarsa a adawa ba ta ba shi kariya daga bincike ko gurfanarwa ba.”
ADC ta zargi APC da kai mata hari
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta yi Allah wadai da wani hari da aka kai mata a taron da ta yi a Legas.
Kakakin ADC na kasa, Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa ba za su zuba ido ana cigaba da kai musu hari a jihohi ba.
Bolaji Abdullahi ya zargi APC da hannu a harin da aka kai musu a coci yana mai cewa jam'iyyar ba ta mutunta wajen ibada.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

