APC Ta Yi Martani bayan Tambuwal Ya Zargi Tinubu da Shirin Ruguza 'Yan Adawa

APC Ta Yi Martani bayan Tambuwal Ya Zargi Tinubu da Shirin Ruguza 'Yan Adawa

  • Jam'iyyar APC ta yi martani ga tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, kan wasu zarge-zarge da ya yi
  • Mai magana da yawun APC na kasa, ya bayyana cewa babu komai a cikin zarge-zargen na Tambuwal face soki burutsu
  • Felix Morka ya ba da tabbacin cewa APC ta fi maida hankali wajen sauke nauyin da 'yan Najeriya suka dora mata na jagorantar su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta yi martani ga tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.

Jam'iyyar APC ta zargi Aminu Tambuwal, da yin ikirarin bogi a kanta da kuma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

APC ta yi wa Aminu Tambuwal martani
Hoton Aminu Waziri Tambuwal a zauren majalisa da Shugaba Bola Tinubu yana jawabi a wajen taro Hoto: Aminu Waziri Tambuwal, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun APC na kasa, Felix Morka, ya fitar a shafinsa na X a ranar Lahadi, 7 ga watan Satumban 2025.

Kara karanta wannan

Tambuwal ya yi fallasa, ya tona makircin Tinubu da APC kan 'yan adawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane martani APC ta yi wa Tambuwal?

Ya ce Tambuwal a wata tattaunawa da aka yi da shi kwanan nan, ya yi zargin cewa shugaban kasa da jam’iyya mai mulki suna shirya makarkashiyar kawo rikici a jam’iyyun adawa.

Felix Morka ya bayyana zargin Tambuwal a matsayin mara tushe, yana cewa hakan ya nuna hali mara kyau da shugabannin adawa suke da shi.

"Abin mamaki ne yadda waɗannan shugabannin adawa irin su Tambuwal, Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai, Peter Obi da Rotimi Amaechi, waɗanda suka rike manyan mukaman siyasa a kasarmu, suka gaza wajen samar da shugabanci mai kyau a jam’iyyunsu."
“Maimakon su maida hankali da kwarewarsu wajen gina jam’iyyun adawa masu karfi, sun karkata kan dora alhaki a kan wasu, suna zargin APC kan abin da yake kuskurensu ne kacokam.”

- Felix Morka

Mai magana da yawun APC ya ce zargin da Tambuwal ya yi na cewa an cinno masa EFCC kwanan nan saboda siyasa, ba komai ba ne face kokarin gujewa gaskiya.

Kara karanta wannan

Wike ko Atiku: Tambuwal ya fadi wanda zai marawa baya don zama shugaban kasa

"Babu ɗan adawa da yake sama da doka, kamar yadda babu wani ɗan kasa da yake sama da doka."

- Felix Morka

APC ta kare Shugaba Tinubu daga zargin Tambuwal
Hoton shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana jawabi Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Abin da APC ta fi maida hankali a kai

Felix Morka ya kara da cewa jam’iyyar mai mulki ta fi maida hankali ne kan tafiyar da gwamnati, kuma ba ta da lokacin tsoma baki kan harkokin cikin gida na jam’iyyun adawa da su ke kokarin rugujewa.

Ya kuma jaddada cewa shugabannin adawa sun gaza wajen gina hadaka mai ma'ana, yana mai cewa ‘yan Najeriya za su sake kin ba su kuri'u a zaɓen shekarar 2027.

ADC ta soki jam'iyyar APC mai mulki

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta kitsa tashin hankali yayin wani taro da ta gudanar a jihar Legas.

Jam'iyyar ADC ta bayyana cewa APC mai mulki na shirya irin wannan tuggun ne saboda tsoron shahara da karbuwar da take samu a kasar nan.

Mukaddashin mai magana da yawun ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa APC ta koma amfani da tashin hankali ta hanyar kai hare-hare a tarurrukan 'yan adawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng