2027: ADC Ta Fadi Tsoron da APC Ta Ji bayan kai wa 'Yan Adawa Hari a Wajen Ibada
- Jam’iyyar ADC ta ce APC na amfani da barazana da tashin hankali saboda tsoron shahararta da ke ƙaruwa a fadin Najeriya
- ADC ta yi zargin cewa ana amfani da ’yan daba wajen rusa tarurrukan jam’iyyar a jihohi daban-daban ciki har da Kaduna da Legas
- APC ta nesanta kanta daga zarge-zargen, tana mai cewa ADC ba barazana ba ce gare ta kuma ba za ta yi amfani da tashin hankali ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Jam’iyyar ADC ta zargi APC da kitsa barazana da tashin hankali saboda tsoron shahararta da ke ƙaruwa gabanin babban zaɓen 2027.
Zargin na ADC ya biyo bayan rikice-rikice da dama da suka faru a tarurrukanta, musamman a Kaduna da Legas, inda ’yan daba suka mamaye wuraren ganawar tare da rusa ayyukan jam’iyyar.

Kara karanta wannan
Tinubu zai kawo tsarin aiki da ba a taba yi ba a Najeriya, komai zai sauya a ofisoshi

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa APC ta nesanta kanta daga waɗannan abubuwa, tana mai cewa ADC ba wata barazana bace da za ta sa ta koma tayar da tarzoma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An farmaki 'yan ADC a Kaduna da Legas
A makon da ya gabata, taron masu ruwa da tsaki na ADC a Kaduna ya gamu da mamayar ’yan daba, lamarin da ya jawo rauni ga wasu daga cikin mahalarta.
Haka kuma, a ƙarshen mako, wani babban taron jagororin ADC a Alimosho, Legas, ya rikide zuwa rikici bayan wasu ’yan daba da ake zargin an ɗauko su ne suka kai farmaki.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ɗan takarar gwamnan Legas a ƙarƙashin LP a 2023, Gbadebo Rhodes-Vivour ya sanar da komawarsa ADC.
Rahotanni sun nuna cewa asalin wurin taron, Lion Field, an rufe shi da jami’an tsaro kafin ADC ta koma wani Coci, inda aka kaddamar da Rhodes-Vivour.
Sai dai har a cikin cocin ma, ’yan daba sun mamaye wurin, abin da ADC ta ce ya nuna APC ba ta mutunta wuraren ibada.
ADC ta ce jam'iyyar APC ta tsorata
Punch ta wallafa cewa Mai magana da yawun ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya ce waɗannan hare-hare sun zama jigo a irin salon mulkin APC a kwanakin nan.
Ya bayyana cewa lamarin ya fara ne a Edo da gargadi ga shugabannin ADC, sannan aka ci gaba da Kogi da Niger, kafin ya tsallaka zuwa Kaduna, Kebbi da kuma Legas.
Bolaji Abdullahi ya ƙara da cewa irin wannan aiki yana da kama da ayyukan ta’addanci da ya kamata a ji kyamar su.

Source: Facebook
Martanin APC kan kai wa ADC hari
Sai dai mai magana da yawun jam’iyyar APC na ƙasa, Bala Ibrahim, ya karyata zarge-zargen da aka musu.
Ya jaddada cewa APC ba ta amfani da tashin hankali wajen siyasa, domin jam’iyyar na da tsari da kuma damar da za ta tabbatar da karfinta ta hanyar dimokuraɗiyya, ba ta hanyar tada rikici ba.

Kara karanta wannan
Tinubu ya amsa kira kan kirkirar 'yan sandan jihohi, ya gano sirrin magance ta'addanci
Ana zargin kaiwa 'yan APC hari a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan APC a Kano sun yi zargin cewa ana kai musu hari a wasu yankunan jihar.
'Dan majalisar wakilai, Alhasan Ado Doguwa ya bayyana cewa suna fuskantar barazana ne a karamar hukumar Tudun Wada.
Biyo bayan haka, rundunar 'yan sandan jihar ta gayyaci wata shugabar karamar hukuma da ake zargi da hannu a wani hari da aka kai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
