‘Bai Fahimci Komai ba’: Tambuwal Ya Fadi inda Tinubu Ke da Matsala a Mulki

‘Bai Fahimci Komai ba’: Tambuwal Ya Fadi inda Tinubu Ke da Matsala a Mulki

  • Tsohon gwamnan Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya soki shugaba Bola Tinubu da gwamnatinsa
  • Tambuwal yana zargin gwamnatin Tinubu da APC da rashin sanin tsarin mulki da yadda ake tafiyar da Najeriya
  • Sanata Tambuwal ya bayyana cewa Atiku Abubakar ya fi Tinubu fahimtar mulki, musamman a batun tsarin mulkin tarayya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya caccaki Bola Ahmed Tinubu da gwamnatinsa a Najeriya.

Tambuwal ya koka kan wasu matakai da ke tabbatar da cewa akwai rashin sanin tsarin mulki a tattare da Tinubu.

Tambuwal ya yi durar mikiya kan gwamnatin Tinubu a Najeriya
Sanata Aminu Waziri Tambuwal da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Aminu Waziri Tambuwal.
Source: Facebook

Tsohon gwamnan Sokoto ya bayyana haka yayin hira da gidan talabijin na Channel a daren jiya Juma'a 5 ga watan Satumbar 2025.

Tambuwal na daga cikin jiga-jigan yan adawa da suke kokarin ganin bayan Tinubu a kan mulki a zaben shekarar 2027da ake tunkara.

Kara karanta wannan

Ta fara tsami tsakanin gwamna da ministan tsaro, APC ta fusata kan lamarin

Tambuwal ya dura kan Tinubu da gwamnatinsa

Yayin hirar, Tambuwal ya ce Tinubu bai ma fahimci komai game da Najeriya ba da tsarin mulkin tarayya.

Ya ce tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya fi shi sanin yadda ake mulki da kuma wasu bangarori da yawa.

A cewarsa:

"Atiku ya fi Bola Tinubu ta bangarori da yawa musamman ta yadda za a mulki jama'a da kuma tsarin mulkin tarayya.
"Shi a kullum yana nuna fifiko zuwa ga yankinsa, Lagos kuma bai fahimci yadda ake gudanar da tsarin mulkin tarayya ba.
"Har yanzu babu jakadun kasashen duniya daban-daban fiye da shekaru biyu kenan da hawa madafun iko."
Tambuwal ya fadi kuskuren da Tinubu ke yi a mulki
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal. Hoto: Aminu Waziri Tambuwal.
Source: Twitter

Sanata Tambuwal ya fadi babbar matsalar Tinubu

Tambuwal ya ce kwata-kwata Bola Tinubu bai ma fahimci yadda Najeriya take ba a matsayin kasa bare ya yi ingantaccen mulki.

Ya ce abin takaici ne yadda gwamnatin ta gagara shawo kan matsalolin da Najeriya take fuskanta.

"Bai iya mulki ba, Tinubu bai ma fahimci ya Najeriya take ba a matsayin kasa saboda rashin sanin yadda zai yi mulki."

Kara karanta wannan

Tambuwal ya yi fallasa, ya tona makircin Tinubu da APC kan 'yan adawa

- Cewar Aminu Waziri Tambuwal

Yadda yan adawa ke shirin kifar da Tinubu

Har ila yau, Aminu Waziri Tambuwal, ya tabo batun kokarin kifar da Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027 duba da yadda suka lalata Najeriya.

Tambuwal ya bayyana cewa yana cikin kokarin da 'yan adawa suke yi shi ne ganin sun raba Tinubu da mulkin Najeriya a zaben 2027 da ke tafe.

Ya bayyana kuskuren da 'yan adawa za su yi wanda zai sanya Tinubu da APC su sake lashe zabe a saukake inda ya ba da shawarwari domin ganin an cimma burin da aka sanya a gaba.

Tambuwal ya yi tone-tone kan gwamnatin Tinubu

A baya, mun ba ku labarin cewa Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya yi maganganu na zargi kan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyar APC.

Tsohon gwamnan Sokoto, Tambuwal ya bayyana cewa rigingimun cikin gidan da suka addabi jam'iyyun adawa ba haka nan banza su ke faruwa ba.

Tambuwal ya bayyana cewa akwai hannun Shugaba Tinubu da jam'iyyar APC wajen kunno rikicin da yake neman lalata jam'iyyun adawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.