'Ana Kai wa 'Yan APC Hari a Kano,' Ado Doguwa Ya Fadi Halin da Suka Shiga

'Ana Kai wa 'Yan APC Hari a Kano,' Ado Doguwa Ya Fadi Halin da Suka Shiga

  • Alhasan Doguwa ya zargi shugabar karamar hukumar Tudun Wada, Sa’adatu Salisu da daukar ’yan daba domin a farmaki mambobin APC
  • 'Dan majalisar ya ce ma’aikata a wani kamfani a Tudun Wada sun samu rauni bayan ’yan daba sun mamaye wurin ranar 28 ga Agusta
  • Rundunar ’yan sanda ta tabbatar da karɓar korafi daga mambobin APC tare da gayyatar shugabar karamar hukumar domin bincike

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Dan majalisar wakilai daga mazabar Doguwa/Tudun Wada, Alhassan Ado Doguwa, ya yi zargin cewa 'yan APC na fuskanatar barazana a Kano.

Ya zargi shugabar karamar hukumar Tudun Wada, Sa’adatu Salisu da hannu wajen kai hare-hare ga mambobin jam’iyyar APC a jihar Kano.

Dan majalisar Kano, Ado Doguwa
Dan majalisar Kano, Ado Doguwa a majalisar wakilai. Hoto: Alhasan Ado Doguwa
Source: Twitter

Doguwa, wanda shi ne shugaban kwamitin harkokin albarkatun man fetur a majalisar wakilai, ya bayyana haka ne a wata hira kamar yadda the Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kano: Ciyaman ta sake jawowa Abba Kabir magana, yan sanda sun gayyace ta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa hare-haren na barazana ga rayuka da kuma zaman lafiyar tsarin dimokuradiyya a jihar.

Zargin kai wa 'yan APC farmaki a Tudun Wada

A cewar Doguwa, a ranar 28 ga watan Agusta ne wasu da ake zargin ’yan daba ne suka mamaye wani kamfani da ke Tudun Wada

Leadership ta rahoto ya ce maharan sun raunata ma’aikata da dama, inda ya ce mafi yawan wadanda suka jikkata mambobin jam’iyyar APC ne.

Shugaban APC na Kano tare da Abdullahi Ganduje a shekarun baya
Shugaban APC na Kano tare da Abdullahi Ganduje a shekarun baya. Hoto: Salihu Tanko Yakasai
Source: UGC

Ya kara da cewa ba wannan ne karon farko da aka kai wa mambobin jam’iyyar tasu hari ba, domin an sha kai musu farmaki a lokuta daban-daban cikin jihar.

“Wannan dabi’a ce ta rashin imani kuma ba za a lamunce ta ba. Duk wanda ya yi irin wannan aiki ya sabawa doka kuma dole ya fuskanci hukunci,”

- In ji shi.

Matakin da ’yan sandan Kano suka dauka

Kakakin rundunar ’yan sanda a Kano ya tabbatar da cewa sun samu korafi daga mambobin APC na karamar hukumar Tudun Wada.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun cinnawa gidaje 30 wuta a Filato, mutum 300 sun shiga garari

Ya ce wadanda abin ya shafa sun hada da shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar, inda suka yi zargin cewa shugabar karamar hukumar ce ta dauki nauyin farmakin.

A cewarsa, an riga an mika goron gayyata ga Sa’adatu Salisu domin ta bayyana a gaban jami’an tsaro.

Alhasan Ado Doguwa ya yi gargaɗi

Doguwa ya yi gargaɗin cewa duk wanda ke rike da madafun iko bai kamata ya rika amfani da matsayinsa wajen cutar da al’umma ba.

Ya ce idan aka bar irin wadannan lamura ba tare da daukar mataki ba, hakan zai iya haifar da barazana ga dimokuradiyyar Najeriya.

Ya kuma bukaci hukumomin tsaro da su yi aiki da gaskiya da adalci domin tabbatar da cewa wadanda ake zargi sun fuskanci hukunci.

Doguwa ya yi nuni da cewa siyasa hanya ce ta hidima ga jama’a, ba hanyar zalunci ko amfani da karfi ba.

An kama masu garkuwa a jihar Kano

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta kama wasu masu garkuwa da mutane a jihar Kano.

Asirin masu garkuwa da mutanen ya tonu ne bayan sun sace wani bawan Allah da ya gane fuskar jagoransu.

Yayin da ya ke amsa tambayoyi a wajen 'yan sanda, shugaban masu garkuwar ya amsa cewa yana da hannu a sace sacen mutane a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng