Wike ko Atiku: Tambuwal Ya Zabi wanda Zai Marawa Baya don Zama Shugaban Kasa
- Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya yi magana kan abubuwan da ya ke dubawa wajen yanke hukunci a siyasa
- Tambuwal ya nuna cewa yana ajiye abokantaka a gefe guda idan ya tashi yanke hukunci kan abubuwan da suka shafi siyasa
- Sanatan ya kuma bayyana wanda zai iya goyon baya don zama shugaban kasa tsakanin Atiku Abubakar da Nyesom Wike
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya bayyana wanda zai marawa baya tsakanin Nyesom Wike da Atiku Abubakar, don zama shugaban kasa.
Aminu Tambuwal ya ce gwara ya marawa Atiku Abubakar baya fiye da Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, don zama shugaban kasar Najeriya.

Source: Twitter
Tambuwal ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin 'Politics Today' na tashar Channels tv a ranar Juma'a, 5 ga watan Agustan 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aminu Tambuwal ya fadi salon siyasarsa
Sanatan mai wakiltar Sokoto ta Kudu ya fayyace cewa zaɓin siyasarsa kullum yana kasancewa bisa ka’ida da maslahar kasa, ba wai bisa kiyayya ta kashin kai ba.
"Ba ku taɓa jin ina sukar Tinubu kan al’amuran kashin kai ba, haka kuma ba ku taɓa jin ina sukar Wike a karan kaina ba."
"Rashin jituwar mu duk bisa ka’ida ne da kuma irin tafarkin da kasar nan take bi."
- Aminu Tambuwal
Tambuwal ya kuma yi waiwaye kan tafiyar siyasarsa, musamman lokacin da ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC a zamanin gwamnatin Goodluck Jonathan.
A cewarsa, wannan mataki ya samo asali ne daga sabanin akida, ba wai saboda kiyayya ba.
"Ba ni da wata matsala da Shugaba Goodluck Jonathan, amma mun samu rashin jituwa, hakan yasa na bar PDP na koma APC."
"Lokacin da nake shugaban majalisar wakilai, sau da dama muna da sabanin ra’ayi kan manufofi, wannan kuwa wani bangare ne na dimokuraɗiyya."
- Aminu Tambuwal
Tambuwal ya fadi zabinsa tsakanin Wike da Atiku
Ya jaddada cewa abokantaka ta kashin kai ba ta shiga lamarin siyasa da yake yanke hukunci a kai.
“Idan Wike da Atiku suka bukaci karbar wayata, zan ba Wike a matsayinsa na abokina. Amma idan batun shugabancin kasa ne, akwai layin da nake shatawa."
- Aminu Tambuwal

Source: Twitter
Ya kara da cewa fifikonsa na Atiku fiye da Wike ba saboda al’amuran kashin kai ba ne, illa dai saboda yana ganin Atiku ya fi cancanta ya jagoranci Najeriya.
“Ko gobe ma, gwara na marawa Atiku baya maimakon Nyesom Wike domin shugabancin wannan kasa."
- Aminu Tambuwal
Tambuwal ya ba 'yan adawa lakanin karya Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana cewa abu ne mai yiwuwa a kifar da APC.
Tambuwal ya bukaci 'yan adawa da su zama tsintsiya madaurinki daya idan suna son yin nasara a kan shugaba Bola Tinubu.
Ya bayyana rashin dunkulewar 'yan adawa a waje guda, zai saukakawa Tinubu samun nasara a zaben 2027.
Asali: Legit.ng

