2027: 'Yan Siyasan Arewa da Suka Rasa Damar Takara saboda kai Tikitin PDP zuwa Kudu
FCT, Abuja - Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta gama yanke shawara kan yankin da take so dan takararta na shugaban kasa ya fito a zaben shekarar 2027.
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jam'iyyar PDP ta kai tikitin takararta zuwa yankin Kudancin Najeriya a zaben shugaban kasa na 2027.

Source: Twitter
PDP ta kai tikitin takara zuwa Kudu
PDP ta tabbatar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin X, bayan kammala taronta na NEC karo na 102, wanda ta gudanar a birnin tarayya Abuja a ranar Litinin, 25 ga watan Agustan 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai magana da yawun PDP, Debo Olugunagba, ya bayyana cewa an cimma matsayar ne bayan NEC ta amince da shawarwarin kwamitin rabon mukamai na jam'iyyar.
Wannan matsayar na nufin cewa yan takara da za su nemi kujerar shugaban kasa a karkashin inuwar PDP, za su fito ne daga yankin Kudancin Najeriya.
Kai tikitin PDP zuwa kudu ya jawo magana
The Punch ta rahoto cewa kungiyar North Central Renaissance Movement, ta nuna rashin amincewa da matakin jam’iyyar PDP na kai tikitin takarar shugaban kasa zuwa Kudu zaɓen 2027.
Shugaban kungiyar, Farfesa K’tso Nghargbu, ya ce a bisa adalci, ya kamata a ba Arewa ta Tsakiya tikitin shugaban ƙasa, domin shi kaɗai ne yankin da bai taɓa samar da shugaban kasa ko mataimakin shugaban kasa ba tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya.
Wani jigon PDP a jihar Sokoto, Yusuf Dingyadi, ya soki matakin kai tikitin zuwa Kudu, yana mai gargadi cewa hakan na iya raunana damar jam'iyyar a zaɓe da kuma rasa magoya baya daga Arewa.
A yayin wata hira da jaridar, Yusuf Dingyadi ya yi gargadin cewa matakin na iya sa mutane da dama daga Arewa su nemi wata jam’iyya daban domin cimma burinsu na siyasa kafin zaɓen 2027.
Sai dai, kungiyar Middle Belt Forum ta fito ta kare matakin PDP na ba yankin Kudu tikitin takarar shugabancin kasa a 2027.
An ji cewa shugaban kungiyar na kasa, Dr Bitrus Pogu, ya ce matakin na PDP adalci ne kuma ya yi daidai da tsarin rabon kujeru na jam’iyyar.
Hakazalika sakataren yada labaran PDP na jihar Kwara, Olusegun Asewara, ya yaba da matakin kai tikitin zuwa Kudu.
'Yan siyasar Arewa da za su rasa damar takara
Matakin PDP na kai tikitin zuwa Kudu, na nufin cewa 'yan siyasar Arewa da ke da burin neman kujerar shugaban kasa, ba za su samu damar yin hakan ba a karkashin inuwar jam'iyyar.
Ga wasu daga cikinsu a nan kasa:
1. Gwamna Bala Mohammed
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, yana da burin yin takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Source: Facebook
Sai dai, wannan matakin na nufin cewa dole ne ya jingine burinsa na yin takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Jaridar TheCable ta ce yayin wata hira da manema labarai a Bauchi, Gwamna Bala ya bayyana cewa ya hakura da yin takarar shugaban kasa, biyo bayan matakin da PDP ta dauka.
Gwamna Bala ya bayyana cewa ya ajiye burinsa na neman shugaban kasa a gefe, domin ci gaban jam’iyyar PDP da haɗin kan Najeriya gaba ɗaya.

Kara karanta wannan
Ministan Tinubu ya hango hadarin da PDP za ta shiga idan ta tsayar da Jonathan takara a 2027
Ya ce ya yanke shawarar janye burinsa na neman shugabancin kasa ne, domin girmama tsarin jam’iyya da kuma ba wasu damar samun adalci wajen cimma burinsu.
2. Gbenga Olawepo-Hashim
Gbenga Olawepo-Hashim na daga cikin 'yan siyasan Arewa da ke da burin yin takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar PDP.

Source: Twitter
Tsohon dan takarar shugaban kasan ya fito ya soki matakin PDP na kai tikitinta zuwa yankin Kudu.
A yayin wata hira da tashar Channels tv, Gbenga Olawepo-Hashim ya ce matakin kai tikitin takarar zuwa Kudi, ba shi da tarihi a PDP tun farko domin babu adalci a ciki ko kadan.
'Dan siyasar da aka haifa a jihar Kebbi ya yi nuni da cewa matakin zai raunana damar PDP ta fitar da ɗan takarar da zai iya fafatawa a zaben 2027.
3. Abubakar Bukola Saraki
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, na daga cikin wadanda ake hasashen za su iya neman takarar shugaban kasa a PDP.

Source: Twitter
A zaben 2023, ya yi takarar shugaban kasa a PDP, amma ya fadi a zaben fitar da gwanin jam'iyyar.
Saraki wanda ya jagoranci kwamitin sulhu na PDP, ya gamsu da matakin jam'iyyar na kai tikitin takarar shugaban kasa zuwa Kudu a 2027.
Wike ya kafawa PDP sharudda
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya gindaya sharuddan zaman lafiya ga jam'iyyar PDP.
Wike ya bayyana cewa dole ne a mutunta bukatunsa idan har ana so ya amince da babban taron jam'iyyar da ake shirin gudanarwa.
Daga cikin bukatun nasa akwai maganar cewa dole ne shugaban jam'iyyar PDP ya fito daga yankin Arewa ta Tsakiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


