'Namadi Ya Zamo Gwarzo,' Jigon APC, Mahmood Ya Jero Alherin Gwamnan Jigawa

'Namadi Ya Zamo Gwarzo,' Jigon APC, Mahmood Ya Jero Alherin Gwamnan Jigawa

  • Wani jigo a jam’iyyar APC, Abdullahi Mahmood, ya bayyana Gwamna Umar Namadi a matsayin gwarzon da Allah ya aiko domin daukaka Jigawa
  • Ya ce gogewarsa a harkokin ilimi, kasuwanci da aikin gwamnati ya taimaka wajen habaka tattalin arzikin jihar cikin gaskiya da rikon amana
  • A cewar Abdullahi Mahmood, shirin Greater Jigawa Agenda na Danmodi ya riga ya fara tasiri a rayuwar talakawa jihar ta fannoni daban-daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar JigawaGwamna Umar Namadi, wanda aka fi sani da Danmodi, ya samu yabo daga wani jigo a jam’iyyar APC, Abdullahi Mahmood.

Kusa a jam'iyyar ta APC ya bayyana shi a matsayin gwarzon da Allah ya aiko domin daukaka Jigawa zuwa sabon matsayi.

Legit ta rahoto cewa Mahmood ya fito ne daga Garun Gabas da ke karamar hukumar Mallam-Madori a jihar Jigawa.

Kara karanta wannan

Minista ya fadi yadda manufofin Tinubu su ka ceto albashin ma'aikata a jihohi 27

Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi
Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi da Mahmood. Hoto: Garba Muhammad/Abdullahi Mahmood
Source: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Dan siyasar ya jaddada cewa Gwamna Umar Namadi ya kawo sauyi mai ma’ana a cikin shekar biyu kacal da ya shafe yana mulkin jihar.

Ya kara da cewa, kokarinsa ya sa Jigawa ta zama jiha mafi saurin bunkasa wajen tara kudin shiga a Najeriya, inda aka samu sama da Naira biliyan 62.6 a shekarar 2024.

Nasarorin Namadi a siyasa da tsare-tsare

Mahmood ya ce Danmodi ya nuna irin jagorancin da jama’ar Jigawa ke fata tun shekaru da dama da suka wuce, wanda ya hada kan kowa, har ma da ‘yan adawa.

Ya bayyana cewa gwamnan ya kafa kyakkyawan tarihi a fagen kirkire-kirkire da tsare-tsaren noman zamani, kiwon lafiya, ilimi, tsaro da inganta rayuwar matasa da mata.

Ya kara da cewa shirin sa na Greater Jigawa Agenda da ya kunshi abubuwa 12, ya riga ya fara tasiri a rayuwar al’umma ta fannoni daban-daban.

Wannan, a cewarsa, ya sanya Danmodi cikin shugabannin da suka fi daukar matakai nagari don kyautata rayuwar talakawa.

Kara karanta wannan

An fasa ƙwai: Hon. Jibrin ya fallasa waɗanda ba su son Kwankwaso ya shiga APC

Mahmood ya ce an gyara ilimi a Jigawa

A bangaren ilimi, ya ce gwamnatin Namadi ta dauki matakan gyara da suka shafi kafa sababbin cibiyoyi da daukar kwararru aiki.

Mahmood ya bayyana cewa an zabi mutane shida masu digirin PhD domin shiga majalisar zartarwa da nufin kawo sauyi a Jigawa.

Baya ga haka, gwamnatin ta dauki malamai 3,000 na J-Teach a matsayin ma’aikatan dindindin, tare da karin wasu 3,000 domin cike gibin da ake da shi.

A cewar Mahmood, gwamna Umar Namadi ya kara tallafin karatu ga dalibai da kashi 100 bayan shirin ilimi kyauta ga 'ya'ya mata.

Ya ce an samar da sababbin ajujuwa 156, an gyara 221, an gina bandaki 40 da rijiyoyin ruwa 68, tare da rarraba kujeru sama da 14,000 ga makarantu a dukkan kananan hukumomi 27 na jihar.

Bangaren noma, lafiya da walwalar jama’a

A bangaren noma, ya ce Danmodi ya rage farashin taki, ya raba injinan gona 54 ga kananan hukumomi da nufin bunkasa samar da abinci.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin baiwa jihar Legas fifiko wajen ayyukan raya kasa

Ya kara da cewa gwamnan ya jawo hankalin kamfanoni 50 da ke shirin zuba jari a harkar noma da ma’adinai a Jigawa bayan samar da motocin noma 54.

A fannin lafiya, gwamnatin ta tallafa wa cibiyoyin lafiya 281 da kudi kai tsaye daga NPHCDA, tare da hadin gwiwar WAMY wajen yi wa marasa lafiya 2,000 aikin ido kyauta da magunguna.

Gwamna Namadi yayin raba tallafi ga wasu matasa a Jigawa
Gwamna Namadi yayin raba tallafin kudi ta ATM ga wasu matasa a Jigawa. Hoto: Garba Muhammad
Source: Facebook

Ayyukan Namadi ga matasa da mata

Mahmood ya ce Gwamna Namadi ya kafa hukumar matasa wacce ta bai wa mata 1,000 tallafin N50,000 domin fara sana’a, tare da tallafa wa matasa 1,500 da irin wannan jari.

Haka kuma an horas da matasa 240 sana’o’i tare da kayan aiki, sannan an tallafa wa kananan masana’antu 1,000 da N100,000 ta shirin J-Cares.

APC ta lashe zaben cike gurbi a Jigawa

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ce ta lashe zaben cike gurbi da aka yi a jihar Jigawa.

Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da zaben ne bayan rasuwar dan majalisa mai wakilatar Garki da Babura.

Zaben na cikin jerin zabubbukan da hukumar INEC ta shirya a sassan Najeriya daban daban domin maye guraben da aka samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng