2027: Tinubu Ya Fadi yadda 'Yan Adawa Suka Saka APC a gaba da Fara Kamfen

2027: Tinubu Ya Fadi yadda 'Yan Adawa Suka Saka APC a gaba da Fara Kamfen

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce jam’iyyun adawa ne suka jawo APC cikin harkar siyasa tun da wuri kafin zaben 2027 ya kankama
  • Ya jaddada cewa ba zai bari siyasa ta shagaltar da shi daga samar da ingantaccen shugabanci ga ‘yan Najeriya ba
  • Gwamnonin Arewa maso Gabas sun kai bukatunsu ga shugaban kasa ciki har da batun tsaro da gina muhimman abubuwan more rayuwa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi zargin cewa jam’iyyun adawa ne ke jawo jam’iyyar APC cikin harkokin siyasa tun kafin lokacin zabe mai zuwa a 2027.

A watan Afrilun da ya wuce ne shugaban kasar ya hana fara masa yakin neman zabe da wasu masoyansa suka fara masa kamfen.

Kara karanta wannan

Minista ya fadi yadda manufofin Tinubu su ka ceto albashin ma'aikata a jihohi 27

Shugaba Bola Tinubu yana wani jawabi a Abuja
Shugaba Bola Tinubu yana wani jawabi a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa shugaban kasar ya fadi haka ne a lokacin da ya karɓi bakuncin gwamnonin Arewa maso Gabas karkashin jagorancin gwamnan Borno, Babagana Zulum.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin sun bayyana aniyarsu ta yin aiki tare da shugaban kasa domin samar da kyakkyawan shugabanci da kuma barin tarihi mai kyau ga kasar nan.

Bukatun gwamnonin Arewa maso Gabas

A yayin ganawar, gwamnonin sun mika bukatu da dama ga shugaban kasa, ciki har da batun yaki da matsalolin tsaro da kuma samar da manyan abubuwan more rayuwa.

Farfesa Babagana Zulum, wanda ya yi jawabi a madadin takwarorinsa, ya bayyana cewa yankin Arewa maso Gabas na fuskantar kalubale na musamman.

The Guardian ta rahoto cewa ya gode wa shugaban kasan bisa ci gaba da goyon bayan da yake bai wa yankin musamman wajen yakar ta’addanci da tabbatar da zaman lafiya.

Tinubu yayin ganawa da gwamnonin Arewa maso Gabas a fadar shugaban kasa
Tinubu yayin ganawa da gwamnonin Arewa maso Gabas a fadar shugaban kasa. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Shugaba Tinubu ya nuna cewa ya fahimci irin ƙoƙarin da gwamnonin yankin suka yi wajen tallafawa jami’an tsaro ta hanyar amfani da CJTF.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa sun gana da Tinubu a Abuja, sun roƙi manyan alfarma 2

Tinubu: Dalilin fara kamfen da wuri

Yayin da ya koma kan batun siyasa, Shugaba Tinubu ya ce jam’iyyun adawa ne suka fara jawo hankalin APC cikin harkokin siyasa tun da wuri.

Sai dai ya bayyana cewa ba zai bari hakan ya shagaltar da shi daga ci gaba da gudanar da shugabanci mai inganci ga al’umma ba.

“Ina mai jaddada cewa ba zan bari siyasa ta shagaltar da ni daga aikin da ya kamata ba. Lokacin siyasa zai zo, amma a yanzu na fi karkata wajen gina Najeriya,”

- In ji shi.

Ya ce APC za ta tabbatar da karfinta a lokacin da ya dace, domin siyasa tana bukatar hakuri da hangen nesa na masu yin aiki fiye da magana.

Dalung ya ce Tinubu zai koma Legas

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon ministan wasanni a lokacin shugaba Muhammadu Buhari, Solomon Dalung ya ce ADC za ta ba da mamaki a 2027.

Kara karanta wannan

"Akwai sauran gurabe": Tinubu ya kwantar da hankalin 'yan kungiyar Buhari

Dalung ya ce ya dace shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya fara shirin komawa gida Legas daga zaben shekarar 2027.

Yana ganin 'yan Najeriya sun gaji da salon mulkin APC da ya jefa su a matsalolin tattali da tsaro kuma za su bukaci sauyi a zabe mai zuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng