Ana Jiran Dawowar Gwamna Fubara a Satumba, APC Ta Gindaya Sharudan Aiki da Shi
- Jam’iyyar APC a jihar Rivers ta yi magana yayin da ake tsammanin dawo da dakataccen Gwamna Siminalayi Fubara
- Shugaban jam'iyyar a jihar, Tony Okocha ya bayyana cewa zabukan kananan hukumomi alama ce ta abin da zai faru a 2027
- Okocha ya bukaci karin mambobin PDP su sauya sheka don samun kwanciyar hankali a jihar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Port Harcourt, Rivers - Yayin da ake sa ran dawowar mulkin dimokuraɗiyya a Rivers, APC ta shimfida sharuda.
Wasu na ganin Gwamna Simi Fubara zai dawo a ranar 18 ga Satumba bayan sanya dokar ta-baci na tsawon wata shida.

Source: Instagram
Rahoton Tribune ya ce jam’iyyar APC ta tabbatar za ta yi aiki da Gwamna Siminalayi Fubara idan ya dawo daga dakatar da shi da aka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An fadi sakamakon zaben kananan hukumomi
A baya, APC ta lashe kujerun shugabancin kananan hukumomi 20 daga cikin 23 a zaben da aka gudanar a makon karshen mako.
Har ila yau, jam'iyyar APC ta shiga har karamar hukumar Siminalayi Fubara inda ta yi masa cin kaca.
Wannan sakamako ya nuna kamar akwai wani shiri tsakanin PDP da APC tun a lokacin zaben fitar da gwani da aka samu sunayen yan PDP a APC.
APC ta magantu kan dawowar Fubara mulki
Sai dai yayin taron manema labarai, shugaban jam’iyyar, Tony Okocha, ya gode wa masu zabe, ya kuma ce jam’iyyar za ta yi aiki da Fubara idan ya dawo.
Ya ce wannan hadin kai ba zai hana jam’iyya sukar gwamna idan ya yi kuskure ba, amma shugabannin za su guji mugayen manufofinsa, cewar Daily Post.
Okocha ya ce:
"Gwamna da aka dakatar zai dawo ofis a ranar 18 ga watan Satumbar 2025, APC za ta yi aiki idan har ya dawo mulki.
"Akwai jihohi da yan majalisa da gwamna ke jam'iyyu daban-daban, saboda haka za mu yi aiki tare da shi.
"Amma ba wai zai sanya mu ja baya kan sukar gwamnatinsa ba idan ta kauce hanya, ciyamomin kananan hukumomi za su yi aiki da shi sai dai idan ya kawo masu matsaloli."

Source: Facebook
APC ta bugi kirji kan zaben 2027
Okocha ya bayyana zabukan kananan hukumomi a jihar a matsayin alama ta 2027, inda APC ta guji wuraren da PDP ke da karfi, ta mayar da hankali kan wuraren da take da karfi.
Ya ce wannan dabara ce ta siyasa, domin Rivers na karkashin PDP, amma yanzu APC na samun karfi bayan rikicin cikin gida ya ruguza jam’iyyar PDP.
Ya kara da cewa:
"PDP tana cikin matsala mutane da yawa suna sauya sheka daga cikinta zuwa wasu zuwa jam'iyyu, muna daga cikin wadanda suka karbi wasu daga cikinsu."
Wike ya magantu kan dawowar Fubara
Mun ba ku labarin cewa ministan birnin Abuja, Nyesom Wike, ya kada kuri'arsa a zaben kananan hukumomin jihar Rivers.
Nyesom Wike ya yaba kan yadda zaben yake gudana cikin kwanciyar hankali da lumana a sassa daban-daban na jihar.
Ministan ya kuma nuna cewa akwai yiwuwar Gwamna Siminalayi Fubara da 'yan majalisar dokokin jihar su koma kan kujerunsu a watan Satumba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

