APC Ta Kare Salon Mulkin Tinubu yayin da Shugabannin Siyasa a Arewa ke Koka wa
- Jam'iyyar APC ta yi gaggawar kawo wa Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu dauki a lokacin da wasu 'yan siyasa su ka taso shi a gaba
- Jam’iyyar, reshen jihar Legas ta bayyana cewa gwamanatin Tinubu ta fi kowace a kasar nan tafiyar da jama'a da adalci ba tare da son kai ba
- Kariyar da APC ta yi na zuwa bayan wasu manyan 'yan siyasa, musamman a Arewa ke zargin Bola Tinubu da nuna kabilanci karara
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Jam’iyyar APC a Jihar Legas ta yaba wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa kafa sabon salo na mulkin haɗa kan jama’a da kuma haɗa ƙasa baki ɗaya.
Mai magana da yawun jam’iyyar a Legas, Mista Seye Oladejo, ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa APC ta kara da cewa shugabancin Tinubu ya cancanci ƙarin goyon bayan ‘yan Najeriya domin ci gaba da mulki lami lafiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta mara wa Bola Tinubu baya
Jam'iyyar APC ta tabbatar da cewa Bola Tinubu ya kawo salon mulki da ya zama abin koyi musamman a wajen gamsar da dukkanin 'yan kasa.
Sanarwar Mista Seye Oladejo ta ce:
“Shugaba Tinubu na gina Najeriya da tare da kowane dan kasa, ba tare da la’akari da kabila, harshe ko addini ba."
Oladejo ya ce a wannan lokaci da dimokuraɗiyoyi da dama a duniya ke fuskantar ƙalubalen rabuwar kai, gwamnatin Tinubu na jagoranci bisa cancanta.

Source: Facebook
Ya kara da cewa jam’iyyar ta yi alfahari da kasance wa tare da Shugaba Tinubu, wanda ya nuna ƙarfin hali da jajircewa wajen kafa mulkin haɗin kai.
Oladejo ya kuma soki abin da ya kira "’yan adawa masu da su ke rude" da suke ƙoƙarin canza labarin haɗin kan da ake gani a fannoni daban-daban na gwamnati.
APC ta ce Tinubu ya ba kowa mukami
Mai magana da yawun APC ya ce Shugaba Tinubu ya kwarewa ta fannin nade-nade da daidaito tsakanin maza da mata a wajen nada mukaman.
APC ta kara da cewa Bola Tinubu ya shigar matasa cikin mulki, da kuma raba ayyukan ci gaba tsakanin yankuna.
Jam'iyyar ta ce:
“Bayan shekaru biyu da shugabancinsa, Shugaba Tinubu ya yi aiki babu kabilanci, addini, yanki, ko jinsi kuma ana ganin yana jagoranci bisa adalci."
Oladejo ya bayyana majalisar ministocin Tinubu a matsayin ɗaya daga cikin mafiya bambanci da ƙwarewa a tarihin dimokuraɗiyyar ƙasar nan.
Oladejo ya ce Tinubu ya bai wa matasa muhimmiyar dama ta hanyar naɗa su a muƙaman manya, musamman a fannonin fasaha, nishadi, makamashi da sauransu.
APC ta yi magana kan takarar Jonathan
A baya, kun ji cewa APC reshen jihar Legas ta bayyana cewa ba ta ganin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan zai iya kayar da Shugaba Tinubu a zaben 2027 mai zuwa.
Jam'iyyar ta ce Najeriya ta wuce yadda ake tsammani, kuma jama'a na buƙatar shugabancin mai hangen nesa ba wai tuna abubuwan da su ka faru a baya ba ko neman zaben Jonathan.
APC ta yi zargin cewa gwamnatin Jonathan ta bar ƙasa a cikin halin rashin tsaro, cin hanci da rashawa, da tabarbarewar tattalin arziƙi, hakan ya sa shakku ya kama jama’a game da cancantarsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


