"Yaudara ce": Wike Ya Taso Peter Obi a Gaba kan Takarar Shugaban Kasa a 2027
- Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ragargaji tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi
- Nyesom Wike ya bayyana cewa alkawarin yin wa'adi da Peter Obi yake yi, ba komai ba ne face yaudara
- Ministan ya nuna cewa Peter Obi yana yaudarar magoya bayansa don har yanzu ya kasa bayyana a jam'iyyar da zai yi takara
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya gargadi Peter Obi, kan alkawarin yin wa’adi ɗaya kacal idan ya zama shugaban kasa.
Nyesom Wike ya bayyana cewa irin waɗannan alkawuran ba gaskiya ba ne kuma yaudara ce.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce Wike ya bayyana hakan ne yayin hirarsa ta wata-wata da ’yan jarida a Abuja a ranar Litinin, 1 ga watan Satumban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Wike ya ce kan Peter Obi?
Ministan ya goyi bayan matsayar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, cewa ba zai yiwu wani ɗan takarar shugaban kasa ya ba da tabbacin cewa zai tsaya ne don yin wa’adi ɗaya kacal.
A cewarsa, yanayin siyasa kan sauya ne idan mutum ya hau mulki, wanda hakan ke sanyawa da wuya a gaza neman wa’adi na biyu.
Ministan ya ce, idan har Peter Obi ya samu damar zama shugaban kasa, yanayin siyasa da abubuwan da ke gudana na iya sauyawa inji rahoton TheCable.
"Ko da kun ba shi kuri’u miliyan shida da ya samu a baya, duk waɗanda suka zaɓe shi za su ci gaba da zaɓensa. Abin da ya faru a 2023 ba zai sake faruwa ba."
"A wannan zamani na kafafen sada zumunta, a wace jam’iyya zai tsaya? LP ce? Ina zai samo waɗannan kuri’u miliyan shida, a karkashin PDP? A karkashin LP? Idan kana neman mulki, ya kamata mutane su san karkashin wace jam’iyya ka ke takara."
“Ya kamata mutane su san jam'iyyar da za ka tsaya. Shin a watan Disamba zai bayyana? Atiku ya ce zai tsaya a ADC, Amaechi ya ce ADC, amma shi har yanzu bai ce a ina zai tsaya ba."

Kara karanta wannan
2027: Wike ya kyale Jonathan, ya fadi mutum 1 da zai rusa PDP idan ya samu takara
- Nyesom Wike
Wike ya ce Peter Obi bai da alkibla
Wike ya jaddada cewa ana yaudarar magoya bayan Peter Obi, domin babu wani shugaban kasa da zai iya cika alkawarin yin wa’adi ɗaya kacal.

Source: Facebook
"A bayyane yake, El-Rufai ya ce a daina cewa za a yi shekaru huɗu kacal, hakan ba daidai ba ne. Ba na so a yaudari ’yan Najeriya, saboda yanayi kan sauya."
"Ta yaya za ka zauna shugaban kasa ya ce maka ‘zan yi shekaru huɗu’ sai ka gaskata shi?"
"Ta yaya za ka ce haka? Wannan ba dai-dai ba ne. Kada ku gaya wa ’yan Najeriya irin wannan labarin, idan ka isa wurin, sai ka fahimci ko za ka nemi wa’adi na biyu ko ma na uku. Wasu ma sun taɓa yunkurin neman wa’adi na uku.”
- Nyesom Wike
Wike ya ba Jonathan shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ba Goodluck Jonathan shawara kan batun yin takara a zaben 2027.
Wike ya bukaci Jonathan da ya hakura da dawowa siyasa don neman kujerar shugaban kasa kamar yadda wasu ke kokarin zuga shi.
Ministan ya bayyana cewa bai kamata tsohon shugaban kasan ya zubar da mutuncinsa ba ta hanyar dawowa siyasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

