Wike Ya Tsoma Baki kan Batun Takarar Jonathan a 2027, Ya Ba Shi Shawara
- Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya shiga sahun masu ba Goodluck Jonathan shawara kan batun yin takara a 2027
- Wike ya shawarci Jonathan da ya ci gaba da rike girman da yake da shi, maimakon ya dawo da kansa cikin harkar siyasa
- Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya nuna cewa masu zuga shi ya nemi takarar shugaban kasa, ba so na gaskiya ke tsakaninsu ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ba tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, shawara kan zaben 2027.
Nyesom Wike ya shawarci Goodluck Jonathan da kada ya shiga takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta ce Wike ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da 'yan jarida a birnin Abuja a ranar Litinin, 1 ga watan Satumban 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana rade-radin Goodluck Jonathan zai yi takara
An dade ana rade-radin cewa Jonathan na iya sake neman kujerar shugaban kasa a karo na biyu a karkashin jam’iyyar PDP.
Sai dai, tsohon shugaban kasan bai taɓa magana kai tsaye kan batun ba.
Wace shawara Nyesom Wike ya ba Jonathan?
Ministan ya shawarci Jonathan da ya ci gaba da rike matsayinsa na dattijon kasa, maimakon ya dawo siyasa.
“Na san Jonathan sosai. Yana jin daɗin yadda ake girmama shi a duniya a matsayin dattijon kasa, kuma na yi imani zai ci gaba da zama a wannan matsayi."
Wike ya kara da cewa waɗanda ke kiran Jonathan ya tsaya takara su ne irin ’yan siyasan da suka yaudare shi a lokacin zaben 2015, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da zancen.
"Mutanen da ke zuga Jonathan, wane karfin siyasa suke da shi? Ashe ba su ne mutanen da suka yake shi a 2015 ba?"

Kara karanta wannan
2027: Wike ya kyale Jonathan, ya fadi mutum 1 da zai rusa PDP idan ya samu takara
- Nyesom Wike
Wike ya soki 'yan siyasan Najeriya
Ministan ya kuma soki halayyar siyasar Najeriya, inda ya ce akasarin ’yan takara da suka sha kaye a zaɓe, ba su iya amincewa da sakamakon zaɓen ba tare da sun zargi hukumar zaɓe ta INEC ba.

Source: Facebook
Wike ya bukaci ’yan siyasa da su yi koyi da tsohon shugaban kasa Jonathan, wanda ya amince da shan kaye a 2015, yana mai jaddada cewa dole ne ’yan Najeriya su daina yin ƙorafe-ƙorafe bayan kowane zaɓe.
"Ku gaya min wane irin zaɓe INEC ta gudanar da ba a yi korafi ba. Akwai wani ɗan takara da ya sha kaye a zaɓe a wannan kasa sannan ya fito ya amince da shan kaye, ban da Jonathan? Ku ambaci guda ɗaya."
- Nyesom Wike
Kungiyar APCMP ta ba Jonathan shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar APCMP ta bukaci tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, kan kada ya fito takara a zaben 2027.
Kungiyar ta bayyana cewa tsohon shugaban kasan ba zai kai labari ba idan y. Yi takara da mai gorma Shugaba Bola Tinubu.
Hakazalika, kungiyar ta cika baki kan cewa babu wani dan sigasa da zai iya kayar da Tinubu idan suka fafata a zabe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

