Kaduna: ADC Ta Goyi bayan El Rufa'i kan Harin 'Yan Daba a Taron 'Yan Adawa

Kaduna: ADC Ta Goyi bayan El Rufa'i kan Harin 'Yan Daba a Taron 'Yan Adawa

  • Jam’iyyar ADC ta zargi rundunar ’yan sandan Kaduna da yunƙurin haramta yin adawa da gwamanti, musamman a jihar Kaduna
  • Kalaman jam'iyyar na zuwa bayan wasu gungun 'yan daba sun kai farmaki a kan taron kwamitin hadin gwiwar 'yan adawa a jihar
  • Jam’iyyar ta nemi bincike na gaskiya, tare da nanata cewa kowane dan kasa yana da izinin ya gudanar da taro a cikin lumana a Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Jam’iyyar gamayyar adawa ta ADC ta zargi rundunar ’yan sandan jihar Kaduna da yunƙurin haramta siyasar adawa bayan taronta ya rikide zuwa tarzoma a Kaduna.

A ranar Asabar wasu da ake zargin ’yan daba ne suka mamaye wurin kaddamar da kwamitin hadakar 'yan adawa a Kaduna, inda suka afka wa mahalarta da adduna, kulake da duwatsu.

Kara karanta wannan

El Rufai ya nuna yatsa ga Uba Sani bayan 'yan daba sun tarwatsa taron ADC a Kaduna

ADC ta caccaki yan sandan kasar nan
Hoton manyan ADC a yayin wani taro a Abuja Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa mai masaukin baki, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya fusata kwarai bayan harin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma yi zargin cewa manyan jami’an ’yan sanda, har da mataimakin kwamishina, sun tsaya suna kallo yayin da ake lalata dikiyoyin jama'a.

ADC ta goyi bayan Nasir El Rufa'i

Daily Post ta wallafa cewa a wata sanarwa da kakakin jam’iyyar ADC a ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Lahadi, jam'iyyar ta bukaci rundunar ’yan sandan Kaduna ta zurfafa bincike.

Bolaji Abdullahi ya yi tambaya kan dalilin da ya sa jami’an ’yan sanda suka zuba idanu yayin da aka kai wa shugabannin jam'iyyun da su ka halarci taron hari.

ADC ta zargi yan sanda da nuna wariya
Hoton Shugaban riko na ADC, David Mark da alamar jam'iyyar ADC Hoto: Atiku Abubakar
Source: Twitter

Ya kuma soki yadda aka hanzarta kiran ADC “’yan siyasar daba” alhali rundunar ba ta gudanar da bincike a kan harin ba.

Bolaji ya ce kundin tsarin mulki ya bai wa ’yan ƙasa ’yancin yin taro lafiya, ba tare da neman izinin ’yan sanda ba.

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya zargi Uba Sani da tura ƴan daba don tarwatsa taronsu a Kaduna

ADC ta soki barazanar rufe taron siyasa

Jam’iyyar ta kuma yi Allah wadai da barazanar da ’yan sanda suka yi cewa za su rufe duk wani taro “ba bisa ka’ida ba,” tana mai bayyana hakan a matsayin danniya.

Bolaji ya jaddada cewa dimokuraɗiyya ba laifi ba ce, amma 'yan sanda na amfani da karfin ikonsu wajen tsaurara ka’idoji ga jam’iyyun adawa, wanda ke kawo cikas ga siyasa.

Ya roƙi ’yan Najeriya da su bijire wa duk wata barazana da tashin hankali da ake nuna wa ’yan adawa a mulkin APC.

Bayan faruwar lamarin, kakakin rundunar ’yan sandan Kaduna, Mansir Hassan, ya bayyana cewa ba a sanar da jami'an tsaro cewa za a yi taron ba.

Ya ce rundunar ta fara bincike a sakatariyar ADC, kuma shugabannin jam’iyyar sun nesanta kansu daga taron tare da tabbatar da jajircewarsu wajen bin doka.

Akwai sabani tsakanin wasu 'yan jam'iyya da mutanen tsohon gwamna Nasir El-Rufai.

An tarwatsa taron 'yan adawa a Kaduna

Kara karanta wannan

Matsala ta tunkaro El Rufai a ADC, jiga jigan jam'iyya sun taso shi a gaba

A baya, mun wallafa cewa rikici ya barke a wajen kaddamar da kwamitin mika mulki na jam’iyyun adawa a Kaduna, a ranar Asabar 30 ga watan Agusta, 2025.

An yi zargin 'yan daba ne suka afka wurin taron da makamai irinsu adduna, sanduna, da duwatsu, suka ji wa mutane rauni kuma suka lalata motocin da aka bari a wurin.

Wasu da suka halarci taron sun ce duk da tashin hankalin da ya barke, jami’an 'yan sanda da aka turo wurin ba su tsoma baki ba; sai dai sun ja gefe kawai suna kallon abin da ke faruwa

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng