APC Ta Yi Wa Gwamna Fubara Tonon Silili a Zaben Kananan Hukumomin Rivers
- Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Rivers (RSIEC) ta gudanar da zaben kananan hukumomi a ranar Asabar, 30 ga watan Agustan 2025
- Jam'iyyar APC ta samu nasara a cikin fiye da kaso biyu bisa uku na kananan hukumomi 23 na jihar Rivers a zaben
- Gwamna Siminalayi Fubara wanda aka dakatar, bai iya kawo nasara ga jam'iyyarsa ta PDP ba, a karamar hukumar da ya fito
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Rivers - Jam'iyyar APC ta lallasa Gwamna Siminalayi Fubara a zaben kananan hukumomin da aka gudanar a jihar Rivers.
Jam'iyyar PDP ta yi rashin nasara a karamar hukumar da Gwamna Siminalayi Fubara ya fito a zaben wanda aka gudanar a ranar Asabar, 30 ga watan Agustan 2025.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an sanar da sakamakon zaben ne a ranar Lahadi, 31 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan
Ta kacame a Rivers: An fitar da sakamakon zaben kananan hukumomi, an gwada kwanji
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta lallasa Fubara a karamar hukumarsa
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Rivers (RSIEC), Michael Odey, ya sanar da sakamakon zaben.
Jam'iyyar APC mai adawa ta lashe zabe a kananan hukumomi 20 daga cikin 23 da ake da su a jihar.
Yayin da jam'iyyar PDP mai mulki ta samu nasara a kananan hukumomi uku, ciki har da Okbio/Akpor, inda ministan babban birnin tarayya Abuja kuma tsohon gwamnan jihar Rivers, ya fito.
Ɗan takarar jam'iyyar APC, James A. James, ya lashe zabe a karamar hukumar Opobo/Nkoro, inda dakataccen Gwamna Siminalayi Fubara, ya fito.
Mista Michael Odey, ya bayyana cewa ɗan takarar APC, James A. James ya samu kuri’u 37,822, wanda hakan ya tabbatar masa da nasara a zaɓen.
Fubara bai fito zabe ba
Rahotanni sun tabbatar da cewa Gwamna Fubara bai halarci zaken karamar hukumar ba.
A lokacin da aka rufe kada kuri’u a ranar Asabar, ba a ga tsohon gwamnan da aka dakatar a rumfar zaɓensa ba.
Rashin ganin Gwamna Fubara a rumfar zaben ya tilasta wa magoya bayansa da abokan siyasarsa barin wurin bayan sun jira na tsawon sa’o’i.

Source: Instagram
An dai dakatar da Fubara da kuma mambobin majalisar dokokin jihar daga mukamansu bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar saboda tabarbarewar rikicin siyasa.
Haka kuma, shugaban kasa ya naɗa tsohon babban hafsan rundunar sojojin ruwa da ya yi ritaya, Vice Admiral Ibok Ete-Ibas, a matsayin shugaban riko na jihar.
Wike ya fadi lokacin dawo da Fubara kan mulki
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan dage dokar ta bacin da aka sanya a jihar Rivers.
Nyesom Wike ya bayyana cewa Gwamna Siminalayi Fubara da 'yan majalisar dokokin jihar da aka dakatar, za su dawo aikinsu da zarar an cire dokar.
Ministan ya nuna cewa za a cire dokar ta bacin ne a ranar 18 ga watan Satumban 2025 lokacin da za ta cika watanni shida da sanyawa.
Asali: Legit.ng
