Ta Kacame a Rivers: An Fitar da Sakamakon Zaben Kananan Hukumomi, an Gwada Kwanji

Ta Kacame a Rivers: An Fitar da Sakamakon Zaben Kananan Hukumomi, an Gwada Kwanji

  • Bayan gudanar da zabe a jihar Rivers, Hukumar RSEIC ta fitar da sakamakon zaben kananan hukumomi
  • PDP mai mulkin jihar ta samu nasara a kananan hukumomi uku kawai, lamarin da ya jawo APC ta fi rinjaye a zaben
  • Gwamna Siminalayi Fubara ya sha kaye a mazabarsa ta Opobo-Nkoro da PDP ke rike da ita, a cewar hukumar zabe

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Port Harcourt, Rivers - Hukumar zaben jihar Rivers (RSEIC) ta fitar da sakamakon zaben kananan hukumomi.

An tabbatar da cewa jam’iyyar APC ta lashe kananan hukumomi 20 daga cikin 23 a zaben da aka gudanar.

An fitar da sakamakon zaben kananan hukumomi a River
Tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike da Siminalayi Fubara. Hoto: Nyesom Wike, Sir Siminalayi Fubara.
Source: Facebook

An gwabza tsakanin APC da PDP a Rivers

Rahoton Punch ya tabbatar da cewa APC ta yi nasara a zaben shugabannin kananan hukumomi da kansiloli da aka gudanar ranar Asabar.

Kara karanta wannan

An zo wajen: Wike ya fadi lokacin da Gwamna Fubara zai dawo kan mulki a Rivers

Jam’iyyar PDP mai mulki a jihar, ta samu nasara a kananan hukumomi uku kacal a zaben da hukumar Rivers RSIEC ta shirya.

Gwamna Siminalayi Fubara ma ya sha kaye a karamar hukumar Opobo-Nkoro, inda RSIEC ta tabbatar da sakamakon a hedikwatar ta Port Harcourt.

Shugababn hukumar RSIEC, Dr. Michael Odey shi ya tabbatar da sakamakon zaben a yau Lahadi 31 ga watan Agustan 2025.

Michael Odey ya tabbatar da hakan ne da ranar yau Lahadi a sakatariyar hukumar da ke kan hanyar Aba a birnin Port Harcourt.

Ɗan takarar jam'iyyar APC, Barrista James A. James shi ya lashe zaben ƙaramar hukumar da Siminalayi Fubara ya fito.

Opobo/Nkoro, ita ce ƙaramar hukumar da dakataccen gwamna, Siminalayi Fubara, ya fito.

Hukumar zaben Rivers ta fitar da sakamakon zaben kananan hukumomi
Ministan Abuja, Nyesom Wike da dakataccen gwamna, Siminalayi Fubara. Hoto: Nyesom Wike, Sir Siminalayi Fubara.
Source: Facebook

Yawan kananan hukumomi da PDP ta ci

Jam’iyyar APC ta nuna ƙarfi a zaɓen da jam’iyyu 17 suka shiga ciki, wanda ya haɗa da PDP, LP da NRM da sauran su, Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa PDP ke son ɗan takarar shugaban ƙasa Kirista saɓanin APC'

Jam’iyyar PDP ta yi nasara a ƙaramar hukumar Obio/Akpor (inda Ministan Abuja, Nyesom Wike ya fito) da Port Harcourt da kuma Ogba/Egbema/Ndoni.

An ce waɗannan kananan hukumomi guda uku suna da ƙarfin siyasa da tattalin arziki fiye da mafi yawan sauran yankunan jihar.

Yawan kananan hukumomi da APC ta ci

Jam’iyyar APC ta lashe sauran kananan hukumomi 20, ciki har da Omuma, Abua/Odual, Andoni, Eleme, Gokana, Khana, Tai, Etche.

Sauran sun hada da Emohua, Asari-Toru, Degema, Akuku-Toru, Oyigbo, Ahoada ta Gabas, Ahoada ta Yamma, Bonny, Okrika, Ikwerre, Ogu/Bolo da Opobo/Nkoro (inda Gwamna Siminalayi Fubara ya fito).

Odey ya ce za a bai wa waɗanda suka ci zaɓen takardar shaidar nasara nan gaba da ake ganin ba zai wuce Litinin 1 ko Talata 2 ga watan Satumba, 2025 ba.

Ya bayyana cewa ɗan takarar jam’iyyar APC ya samu ƙuri’u 37,822 wanda hakan ya tabbatar da nasararsa a wannan zaɓe.

Wike ya fadi lokacin da Fubara zai dawo

Mun ba ku labarin cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya kada kuri'arsa a zaben kananan hukumomin jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Surutu ya kare, PDP bayyana yankin da za ta dauko dan takarar shugaban kasa a 2027

Nyesom Wike ya yaba kan yadda zaben yake gudana cikin kwanciyar hankali da lumana a sassa daban-daban na jihar.

Ministan ya kuma nuna cewa akwai yiwuwar Gwamna Siminalayi Fubara da 'yan majalisar dokokin jihar su koma kan kujerunsu a watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.