2027: Jerin Wadanda Ake Ganin Za Su Iya Zama Mataimakan Shugaban Kasa daga Arewa

2027: Jerin Wadanda Ake Ganin Za Su Iya Zama Mataimakan Shugaban Kasa daga Arewa

  • Jam'yyar PDP ta zabi ta baiwa Kudu tikitin shugabancin kasa a 2027, lamarin da ya mayar da hankali kan wasu jiga-jigai
  • Masu yiwuwar zama mataimakan shugaban kasa daga Arewa sun fito, ciki har da Gwamna Bala Mohammed
  • PDP na fuskantar kalubale tsakanin hadin kai, karɓuwa ga jama’a, da biyayya ga jam’iyya, wanda zai tantance nasararta a 2027

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Hankali ya koma kan kujerar mataimakin shugaban kasa bayan jam’iyyar PDP ta baiwa Kudu tikitin shugabancin kasa a 2027.

An fara hasashen wasu jiga-jigai daga Arewacin Najeriya da za su iya samun takarar mataimakin shugaban kasa.

PDP ta kare matakin tura tikitin shugaban kasa zuwa Kudu
Jonathan, Peter Obi da Makinde na daga cikin wadanda za su iya takara a 2027. Hoto: Peter Obi, Seyi Makinde, Goodluck Jonathan.
Source: Facebook

Rahoton Vanguard ya ce sunaye uku ne ke kan gaba a matsayin wadanda za su yi takara a zaben shugaban kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matakin PDP kan tikitin takarar shugaban kasa

Hakan ya biyo bayan mika tikitin takarar shugaban kasa zuwa Kudancin Najeriya game da zaben shekarar 2027.

Kara karanta wannan

2027: ADC ta shiga sahun masu zawarcin Jonathan don yin takarar shugaban kasa

Wannan mataki ya kara tabbatar da cewa dole dan takarar mataimakin shugaban kasa zai fito daga Arewacin Najeriya.

Har ila yau, dole dan takarar zai kasance Musulmi domin kawo daidaito game da zaben shekarar 2027 da ke tafe.

Ana hasashen masu neman takara a 2027

Wadanda ake hasashen ba takara sun hada da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi da gwamnan Oyo, Seyi Makinde.

A halin yanzu, masu yuwuwar zama mataimakan shugaban kasa daga Arewa sun fara bayyana, don cike gurbin da PDP ta ware ga yankin.

Tikitin mataimakin shugaban kasa daga Arewa zai kasance muhimmin abu wajen kawo hadin kai da kuma jan hankalin jama’a, cewar Punch.

Wadanda aka iya zama mataimakan shugaban kasa

Bayan mika tikitin ga Kudu, hakan na nufin samun dan Arewa Musulmi mai karfi domin nasarar jam'iyyar PDP.

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi da Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo sun fito a matsayin zabin da ya fi dacewa.

Duk da yake ana danganta Aminu Tambuwal da kawance da jam’iyyar ADC, zai iya zama zabi mai karfi idan ya sake juyowa ga jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

2027: APC ta cika baki kan yiwuwar takara tsakanin Jonathan da Shugaba Tinubu

Peter Obi idan ya juyo PDP, zai bukaci abokin tafiya da zai hada karfinsa da jama’a da kuma samun karbuwa a yankunan karkara a Arewa.

An fara hasashen wadanda za su zama mataimakan shugaban kasa
Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo, Gwamna Bala Mohammed da Aminu Waziri Tambuwal. Hoto: Ibrahim Hassan Dankwambo, Aminu Waziri Tambuwal.
Source: Facebook

2027: An fara maganar mataimakin shugaban kasa

Makinde a matsayinsa na dan Kudu maso Yamma Kirista, shi ma zai bukaci mataimaki Musulmi daga Arewa da zai kara masa karfi a kasa.

Idan aka zabi Dankwambo tare da shi, hakan zai nuna sabon ƙarni na kwararru da ke neman mayar da PDP gaba da APC.

Zabin mataimakin shugaban kasa daga Arewa zai taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tikitin jam’iyya mai karbuwa ko sake shiga cikin rarrabuwar kai.

Gwamna Bala ya magantu kan tsayar da Kirista

Kun ji cewa Gwamna Bala Mohammed ya ce PDP ta koyi darasi daga kuskuren APC a 2023, inda jam’iyyar ta tsayar da tikitin Musulmi da Musulmi.

Sanata Bala ya bayyana cewa PDP ta tura tikitin takarar shugaban kasa zuwa Kudancin Najeriya domin tabbatar da samun adalci.

A cewarsa, hakan zai bai wa jam’iyyar damar hada kan Kiristoci daga Kudu da Musulmi daga Arewa domin samun goyon baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.