'Ba Ruwanmu,' ADC Ta Juya wa El Rufai baya kan Taron da Ya Jawo Rikici a Kaduna

'Ba Ruwanmu,' ADC Ta Juya wa El Rufai baya kan Taron da Ya Jawo Rikici a Kaduna

  • Rundunar ’yan sanda a Kaduna ta fara bincike kan wani taron siyasa da aka ce yana da alaka da tsohon gwamna, Nasir El-Rufai
  • DSP Mansir Hassan ya bayyana cewa taron da ba a sanar da jami’an tsaro ba ya rikide zuwa tashin hankali da harbe-harben ’yan daba
  • Shugabannin jam’iyyar ADC sun musanta sanin komai game da taron, suka kuma nesanta kansu daga duk wani taron El-Rufai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Rundunar ‘yan sandan Kaduna ta ce ta kaddamar da bincike kan wani taron siyasa da aka ce yana da alaka da tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai.

Kamar yadda rundunar ta bayyana, rikici da harbe-harbe sun barke a taron siyasar da aka ce an shirya shi karkashin jam’iyyar ADC ba tare da sanar da jami’an tsaro ba.

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya zargi Uba Sani da tura ƴan daba don tarwatsa taronsu a Kaduna

'Yan sanda sun fara bincike kan taron siyasar da aka alakanta da El-Rufai da ya rikide zuwa tarzoma
El-Rufai da gunguna wasu 'yan siyasa da jami'an tsaro a yayin halartar wani taro. Hoto: Israel Bulus
Source: UGC

Rikici ya barke a taron 'siyasar El-Rufai'

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Mansir Hassan, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar ya ce an fara cikakken bincike, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

DSP Mansir Hassan ya ce duk da gargadin da aka sha yi, masu shirya taron sun ci gaba da gudanar da taron, abin da ya ba wa ‘yan daba damar haddasa tashin hankali.

A cewarsa, binciken farko ya nuna cewa “’yan daba da ke da alaka da tsohon gwamnan” sun rika harbe-harbe a taron, wanda ya tarwatsa zaman lafiya a jihar.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Binciken farko ya nuna cewa taron ya rikide zuwa tarzoma, inda ‘yan daba da masu laifi na siyasa da ke da alaka da tsohon gwamnan suka bude wuta, suka haddasa tashin hankali da tarwatsa zaman lafiya a jihar.”

ADC ta juya baya kan 'taron siyasar El-Rufai'

DSP Hassan ya jaddada cewa rundunar ba za ta kyale duk wanda aka gano yana da hannu a lamarin ba, ko da kuwa yana da girman matsayi, domin babu wanda ya fi karfin doka.

Kara karanta wannan

Matsala ta tunkaro El Rufai a ADC, jiga jigan jam'iyya sun taso shi a gaba

Ya kuma bayyana cewa an tuntubi shugabannin jam’iyyar ADC don fayyace lamarin, inda jami’an jam’iyyar suka musanta shirya taron, suka kuma nesanta kansu daga duk wani abu da aka alakanta da El-Rufai.

Jaridar ThisDay ta rahoto sanarwar ta bayyana cewa:

“Bincike yana gudana, kuma duk wanda aka gano da hannu, ba tare da la’akari da mukami ko matsayin sa ba, zai fuskanci cikakken hukuncin doka.
"Shugabannin jam’iyyar ADC sun tabbatar da jajircewarsu wajen bin doka da oda, tare da nesanta kansu daga ikirarin masu shirya taron.”

An haramta wasu tarukan siyasa a Kaduna

Hassan ya gargadi masu otal-otal, cibiyoyin taro da makamantansu, da su rika tace duk wani taron siyasa da aka zo yi a wajensu, ko kuma su fuskanci hukunci idan tarzoma ta tashi.

Ya ce:

“Duk wani otal, cibiyar taro ko makamancin haka da ya dauki bakuncin taron siyasa ba tare da sanar da ‘yan sanda ko sauran jami’an tsaro ba, shima zai fuskanci hukunci.

Rundunar ta kuma sanar da cewa an dakatar da duk wasu tarukan siyasa da ba a amince da su ba a fadin jihar har sai an tabbatar da an bi doka da kuma tsare-tsaren tsaro yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

KamfaninTeckopi ya ba matasa 20 horo kan adabi da zane a jihar Gombe

El-Rufai ya zargi Uba Sani kan taron Kaduna

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Malam Nasir El-Rufa’i ya yi zargin cewa gwamnatin Uba Sani ce ta shirya kai hari a taron adawa ƴan adawa a Kaduna.

Furucin tsohon gwamnan ya biyo bayan wani hari da ƴan daba su ka kai wa taron haɗin gwiwa na jam'iyyun adawa a jihar a ranar Asabar.

Da ya ke mayar da magana a fusace, Nasir El-Rufa'i ya sha alwashin kawo ƙarshen gwamnatin APC a Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com