Matsala Ta Tunkaro El Rufai a ADC, Jiga Jigan Jam'iyya Sun Taso Shi a Gaba
- Nasir Ahmed El-Rufai na ci gaba da kokarin gina tafiyar hadaka domin ta tsayu da kafafuwanta a jihar Kaduna
- Sai dai, waau jiga-jigan jam'iyyar ADC, ba su gamsu da yadda tsohon gwamnan jihar yake tafiyar da al'amuran siyasar ba
- Sun zarge shi da kokarin kawo rudani a jam'iyyar tare da kwace iko, ta yadda sai abin da yake so za a rika yi a jam'iyyar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Wasu jiga-jigan jam’iyyar ADC a Kaduna sun taso Malam Nasir El-Rufai a gaba.
Jiga-jigan na ADC sun zargi Nasir El-Rufai, da kokarin hargitsa jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.

Source: Twitter
Jiga-jigan na ADC sun bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai ranar Asabar, 30 ga watan Agustan 2025 a Kaduna, cewar rahoton jaridar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manyan ADC na takun saka da El-Rufai

Kara karanta wannan
Dakarun sojoji sun toshe kofofin tsira ga 'yan ta'addan Boko Haram, an kashe miyagu
Adamu Dattijo ya yi magana a madadin jagorori daga kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna.
Ya ce El-Rufai da magoya bayansa suna yin abubuwa masu hadari waɗanda za su iya raunana jam’iyyar ADC, rahoton The Sun ya tabbatar.
Adamu Dattijo ya zargi El-Rufai tare da tsofaffin hadimansa Ja’afaru Sani da Bashir Sa’idu da cewa suna lalata tsarin jam’iyyar domin amfanin kansu da na magoya bayansu.
Ya ce tsohon gwamnan na yin watsi da shugabancin jam’iyyar, inda ya maye gurbin hanyoyin dimokuraɗiyya da abin da ya kira salon mulkin danniya.
"Shi kadai yake kidansa yake rawarsa. Yana ɗaukar matakai ba tare da shawara da kowa ba, sannan ya kan yi taro ne kawai da magoya bayansa musamman waɗanda suka rage a SDP."
"Yayin da yake ware sahihan shugabannin ADC a kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna."
- Adamu Dattijo
Adamu Dattijo ya bayyana wannan salo a matsayin cin mutunci ga makomar jam’iyyar.
"Ana gina jam’iyya ta siyasa ne a kan haɗin kai, shawara, da aminci ga tsarinta — ba a kan son rai na mutum guda ko wasu tsiraru daga cikin magoya bayansa ba."

Kara karanta wannan
'Yan daba sun tarwatsa taron ƴan adawa da El Rufa'i ya halarta a Kaduna, an ji raunuka
- Adamu Dattijo

Source: Twitter
Ana zargin El-Rufai da shirin kwace ADC
Shugabannin sun kuma zargi El-Rufai da shirin kwace tafiyar hadaka a Kaduna ta hanyar kafa shugabannin rikon kwarya daga jam’iyyu daban-daban ba tare da sanin shugabannin ADC ba.
Adamu Dattijo ya ce irin waɗannan shirye-shiryen na nufin dora shugabannin bogi a ADC tare da kwace ikon sahihan shugabanni.
El-Rufai ya magantu kan yin takara
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya tabo batun yin takara a zaben shekarar 2027.
Nasir El-Rufai ya bayyana cewa bai da wani buri na neman mukamin siyasa a 2027, domin ya yi ritaya bayan kammala wa'adin mulkinsa.
Tsohon gwamnan ya ce bai dawo siyasa don neman mulki, sai don ya taimakawa shugabanni na kirki wadanda za su iya kawo ci gaba a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng