‘Ka da Ka Sake ba Fulani Mukami’: Malami Ya Shawarci Tinubu, Ya Fadi Dalilai

‘Ka da Ka Sake ba Fulani Mukami’: Malami Ya Shawarci Tinubu, Ya Fadi Dalilai

  • Kungiyar LND ta yi martani kan ikirarin Fasto Ayodele cewa Fulani za su ci amanar Bola Tinubu, tana karyata maganar
  • Kungiyar ta bayyana Fulani a matsayin mutanen da suka taka muhimmiyar rawa wajen gina Najeriya tare da bayar da misalai daga tarihi
  • Hakan ya biyo bayan kalaman Fasto Ayodele da yake shawartar Tinubu ka da ya sake ba Fulani mukami a gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kungiyar League of Northern Democrats (LND) ta yi martani mai zafi ga Fasto Elijah Ayodele kan kalamansa game da Fulani.

Kungiyar ta yi watsi da maganar shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual wanda ya yi ikirarin Fulani masu cin amana ne.

Fasto ya ba Tinubu shawara kan nada Fulani mukami
Fasto Elijah Ayodele ya sha yin magana kan mulkin Tinubu da zaben 2027. Hoto: Primate Elijah Ayodele, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Gargadin Fasto ga Tinubu game da Fulani

A kwanan nan, Ayodele ya shawarci Shugaba Tinubu kada ya ba Fulani mukamai masu muhimmanci saboda za su ci amanarsa, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

'Na shirya rungumar zaman lafiya': Bello Turji ya dauki alkawari, ya fadi sharrin da ake yi masa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ta bayyana cewa wannan ikirari ba wai karya ce kawai ba, har ila yau yana ƙoƙarin raba kan al’ummar Najeriya.

Ta ce Ayodele yana yada akidar ƙabilanci wanda zai iya haddasa rikici da rashin jituwa tsakanin ’yan kasa.

A wata sanarwa da Dokta Umar Ardo, ya fitar, LND ta ce Fulani ba su taɓa zama masu cin amana ba.

Maimakon haka, tarihi ya nuna su a matsayin mutane masu aminci da kishin kasa.

An ba da misalin gudunmawar Fulani a Najeriya

Kungiyar ta kawo misalai daga tarihin Najeriya, tana nuna irin gudummawar Fulani ga ci gaban ƙasa.

Ta ambaci Sir Ahmadu Bello wanda ya gina Arewacin Najeriya da kyakkyawan shugabanci.

Haka kuma ta kawo misalin Janar Murtala Muhammad wanda ya rasa ransa saboda ƙasar nan, da sauran malamai, sojoji, da shugabanni da suka yi hidima da aminci.

An caccaki Fasto kan neman hada Fulani da Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu yayin taro. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Shawarar da aka ba malaman addini a Najeriya

Kara karanta wannan

Siyasar Sanatan APC da ministan Tinubu na fuskantar matsala, an bukaci su ja baya

LND ta bayyana maganganun Ayodele da cewa ba daga sama ba ne, illa kalaman ƙiyayya da ƙabilanci da aka lullube cikin sunan malanta, ta ce hakan haɗari ne ga haɗin kai.

Kungiyar ta bayyana cewa shugabannin addini wajibi ne su haɗa kan jama’a da yin wa’azi na zaman lafiya, ba su ta da fitina da rarraba mutane ba.

Haka kuma ta jaddada cewa ba daidai ba ne a yi wa kowane ƙabila sharri, ko da kuwa Yarbawa, Igbo, ko Fulani.

LND ta yi kira ga shugabanni da jama’a gaba ɗaya su yi watsi da irin wannan magana, tare da yin ƙoƙari wajen gina ƙasa bisa adalci da cancanta.

A ƙarshe, kungiyar ta ce Fasto Ayodele ya kamata ya nemi gafara ga Fulani da Najeriya baki ɗaya, domin maganarsa akwai son zuciya.

Fasto ya shawarci Tinubu kan zaben 2027

Mun ba ku labarin cewa limamin kirista, Elijah Ayodele ya gargadi Bola Tinubu kan zargin sauya mataimakinsa, Kashim Shettima.

Ayodele ya kuma yi magana kan tazarcensa, ya ce Amurka na “daura damara” domin ganin an cire shugaban daga mulki.

Malamin ya ja kunnen Tinubu ka da ya canza Shettima, ya ce hakan zai zama babbar illa da jawo masa makiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.