Jonathan Ya Hakura da Neman Takarar Shugaban Kasa a 2027? An Samu Bayanai

Jonathan Ya Hakura da Neman Takarar Shugaban Kasa a 2027? An Samu Bayanai

  • An fara yada rahoton cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya hakura, ba zai amsa kiran masu neman ya fito takara a zaben 2027 ba
  • Masu yada labarin sun yi ikirarin cewa Jonathan ya dauki wannan matsaya ne saboda ba ya so a yi amfani da shi wajen raba kan yanin Kudu
  • Dan uwan tsohon shugaban kasar, Azibaola Robert ya musanta rahoton, yana mai cewa babu inda Jonathan ya ce ba zai nemi takara a 2027 ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bayelsa - Tsohon shugaban ƙasa, Dr. Goodluck Jonathan, ya karyata rahotanni da ke cewa ya janye niyyarsa ta tsayawa takarar shugabancin ƙasa a zaɓen 2027.

Wannan karin bayani ya biyo bayan wani rahoto da ya yi ikirarin cewa tsohon shugaban ƙasar ba zai amsa kiran masu neman ya dawo ya nemi mulki ba.

Kara karanta wannan

Reno Omokri: Tinubu ya kawo tsaro a Abuja zuwa Kaduna da ke fama da 'yan ta'adda

Tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Jonathan.
Hoton tsohon shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan Hoto: Azibaola Robert
Source: Facebook

A rahoton da Vanguard ta tattaro, an ce Jonathan ya yanke shawarar ba zai fito takara ba domin kada ya kawo cikas ga haɗin kan yankin Kudu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jonathan ya amince zai fito takara a 2027?

Duk da har kawo yanzu Dr. Jonathan bai fito ya bayyana shirinsa na tsaya wa takara a hukumance ba, amma majiyoyi daga kusa da shi sun nuna ya fara tuntubar 'yan siyasa a kasar nan.

Alamu dai sun nuna Jonathan na da niyyar dawowa fagen siyasa kuma ya nemi zama shugaban kasa, sai dai ba a san wace jam'iyyar zai yi takara a ciki ba.

A yau, ranar Juma’a da rana, ɗan uwansa, Azibaola Robert, ya fito a shafinsa na Facebook, ya karyata rahoton cewa tsohon shugaban kasar ba zai yi takara a 2027 ba.

Ya jaddada cewa babu inda aka ji tsohon shugaban kasar ya ce ba zai tsaya takara a babban zabe mai zuwa ba.

Kara karanta wannan

Borno: Mayakan boko haram sun yi wa matafiya kwantan bauna, sun bude wa motarsu wuta

Jonathan ba zai amsa kiran fitowa takara ba?

Azibaola ya mayar da martani ne ga wani labari da ake yadawa mai taken, “Jonathan ya hakura da takara a 2027, ya ce ba za a yi amfani da shi wajen raba kan Kudu ba.”

Ya bayyana wannan labari a matsayin ƙarya, tare da roƙon ’yan Najeriya da su yi watsi da shi.

Ya kuma ƙara da cewa mutumin da aka bayyana a matsayin “hadimin Jonathan” a cikin rahoton ba shi da alaka da tsohon shugaban kasar.

Tsohon shugaban kasa, Jonathan.
Hoton Jonathan a zaune a wurin wani taro Hoto: Dr. Goodluck Jonathan
Source: Getty Images

A cewarsa, duk da cewa Jonathan bai bayyana niyyarsa ta tsayawa takara ba tukuna, amma kuma bai ce ya janye daga batun neman mulkin ba.

Azibaola ya ce:

"Karya de, babu wata sanarwa a hukumance kan haka, ba ina tabbatar da cewa Jonathan zai fito takara ba ne, amma bai ce ba zai fito ba, ya kamata a kula, mutane na yada labaran karya."

PDP na kokarin dawo da Jonathan da Obi

Kara karanta wannan

Gwamna ya jero mutum 2 da PDP ke tunanin tsaida wa takarar shugaban kasa a 2027

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Bauchi ya ce PDP na duba yiwuwar jawo Goodluck Jonathan da Peter Obi su dawo cikinta domin tunkarar zaben 2027.

Gwamna Bala Mohammed, wanda shi ne shugaban gwamnonin PDP ya ce Jonathan na daya daga cikin yan siyasar da suka fi farin jini a yanzu.

Ya kuma bayyana cewa Obi, wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023 karkashin jam’iyyar LP, zai samu dama idan ya dawo PDP.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262