Kwankwaso Ya Rufe Bakin Masu Yada Jita Jitar Zai Koma Jam'iyyar APC kafin Zaben 2027
- Tsohon dan takarar shugaban kasa a inuwar NNPP, Rabiu Kwankwaso ya kawo karshen rade-radin da ake yi cewa zai canza jam'iyya
- Tsohon gwamnan na jihar Kano ya musanta rahotannin da ake yadawa, ya ce yana jin dadi da farin ciki a jam'iyyar NNPP mai adawa
- A taron NEC da aka gudanar a Abuja, jam'iyyar NNPP ta dauki matsaya kan wanda zai mata takarar shugaban kasa a zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Jagoran NNPP na kasa kuma tsohon gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya ce yana jin dadin zama a jam'iyyarsa, don haka ba ya shirin sauya sheka.
Kwankwaso, wanda ya yi takarar shugaban kasa a inuwar NNPP a zaben 2023, ya tabbatar da cewa babu wani kawance da suka kulla da wata jam'iyya a halin yanzu.

Source: Twitter
Madugun Kwankwasiyya ya bayyana haka ne da yake jawabi a taron kwamitin zartarwa (NEC) na NNPP ta kasa wanda ya guda a Abuja, rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rabiu Kwankwaso na shirin ficewa daga NNPP?
Kwankwaso ya karyata jita-jitar da ke cewa yana shirin sauya sheƙa ko hada kawance da wata jam'iyya, sai dai ya ce a shirye suke ga duk mai son tattauna wa da su.
“Mutane da dama sun yi tunanin yau zan sanar da ko zan ci gaba da zama a NNPP ko zan koma wata jam’iyya.
Amma hakan ba shi ne manufar wannan taron ba. Muna da jam’iyyarmu, kuma muna jin dadin zama a cikinta,” in ji Kwankwaso.
NNPP za ta shiga tattaunawar kulla kawance
Ya ƙara da cewa jam’iyyar NNPP ba ta gaggawa a al'amuranta, amma kofarta a bude take ga duk mai son tattaunawa da ita, rahoton BBC Hausa.
"Mun san cewa za mu ba da gudummuwa a matakin kasa, a shirye muke mu tattauna da duk wanda yake son tattauna da mu domin hadin gwiwa.
An dade ana jita-jitar cewa Kwankwaso zai koma APC mai mulki har wasu na rade-radin Tinubu zai dauke shi a matsayin abokin takara a 2027.
NNPP za ta kara ba Kwankwaso takara?
A jawabinsa, shugaban NNPP na kasa, Dr. Ajuji Ahmed, ya sake tabbatar da cewa Kwankwaso shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a shekarar 2027.
"Sanata Kwankwaso, jagoranmu mai hangen nesa, tsohon gwamna, minista, jakada, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023, shi ne In sha Allah ɗan takarar mu a 2027,” in ji Ahmed.
Ya bayyana NNPP a matsayin “amaryar siyasar Najeriya”, yana mai cewa ita ce jam’iyyar da ake kauna da muradi fiye da kowacce a yanzu.

Source: Facebook
Ajuji Ahmed ya yabawa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, saboda yadda ya “tallafi rayuwar miliyoyin mutane” tare da dawo da zaman lafiya a jihar
A cewarsa, ayyukan da Gwamna Abba ya yi a Kano babbar nasara ce da ke nuna hangen nesa da manufar NNPP na gina sabuwar Najeriya.
Kwankwaso ya cika baki kan Kwankwasiyya

Kara karanta wannan
"Tinubu ba zai iya ba," Babban Malami ya fadi wanda ya dace da mulkin Najeriya a 2027
A wani labarin, kun ji cewa Kwankwaso, ya bugi kirjin cewa babu wani da zai iya kawo matsala ga tafiyar siyasar Kwankwasiyya a jihar Kano.
Tsohon gwamnan na Kano ya ƙara da cewa akidar tafiyar ta kafu ne kan gina ɗan adam da ilimi, kuma ta yi matukar karɓuwa a tsakanin al’umma.
Kwankwaso ya bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf da sauran gwamnoni a fadin kasar da su zuba jari sosai a ilimi da tabbatar ci gaban dan Adam.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

