El Rufa'i Ya Yi Magana kan Tsayawa Takara a 2027, Katin Zabe da Kifar da Tinubu
- Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya ce ba shi da niyyar tsayawa takarar kowace kujera a zaben 2027
- Ya bayyana cewa dalilinsa na dawowa harkar siyasa shi ne kawai don tallafawa shugabanci nagari a matakin jiha da na kasa
- Nasir El-Rufa’i ya yi kira ga matasa da mata su rungumi rajistar katin zabe domin samun damar canza shugabanci a Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya ce ba shi da wani buri na neman mukami a zaben 2027, domin ya kammala shirin yin ritaya daga siyasa bayan mulkinsa.
Ya ce dalilin komawarsa harkar siyasa kawai shi ne don tallafawa shugabannin kirki da za su iya kawo cigaba, ba wai don ya tsaya takara ko neman kujera ba.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa El-Rufa’i ya fadi haka ne a Kaduna, lokacin da ya karɓi wasu matasan jam’iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar ADC karkashin jagorancin Aliyu Bello.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2027: Nasir El-Rufa’i ba zai yi takara ba
El-Rufa’i ya yi Allah-wadai da gwamnatin da ke mulki yanzu, inda ya ce al’ummar Najeriya sun riga sun fahimci gazawarta.
A cewarsa:
“Ina gaya muku, ba zan tsaya takarar komai ba. Ba na son zuwa majalisar dattawa, ba kuma zan tsaya neman kujera ba.
"Dalilin komawa ta harkar siyasa kawai shi ne mu haɗa kai mu fatattaki azzalumai daga shugabanci.”
Ya ce burinsa yanzu shi ne goyon bayan mutanen da ke da kishin kasa da manufofi na gaskiya, musamman matasa da mata masu hangen nesa.
Dalilin dawowar El-Rufa’i fagen siyasa
Vanguard ta rahoto cewa tsohon gwamnan ya ce da farko burinsa bayan barin mulki shi ne ya huta daga duk wata hulɗar siyasa.

Kara karanta wannan
'APC da PDP sun tafka kuskure, da yiwuwar su sha kaye a zaben shugaban kasa na 2027'
Sai dai ya ce abubuwan da ke faruwa a Najeriya sun sa ya sake shiga harkar siyasa, domin a cewarsa, idan ya yi shiru, matsalolin shugabanci ba za su gyaru ba.
“Ina ganin dole mu taka rawa wajen tabbatar da shugabanci nagari a wannan kasa. Shi ya sa na koma siyasa ba tare da wani buri na kaina ba,”
In ji shi.

Source: Facebook
Kiran El-Rufa’i kan katin zaben 2027
El-Rufa’i ya yi kira ga matasa da mata su yi rajistar katin PVC su kuma shiga harkar zabe sosai domin su kasance masu tasiri a zabe mai zuwa.
Ya ce:
“A wasu jihohi kamar Legas da Osun, an yi rajistar mutane sama da 600,000 amma a Kaduna mutum 60,000 kacal suka yi rajista. Wannan ya nuna akwai sakaci a wajenmu.”
Ya jaddada cewa rajistar zabe ita ce hanya mafi muhimmanci da za ta bai wa al’umma ikon zaɓar shugabanni nagari.
INEC ta yi magana kan katin zabe
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta fitar da bayanai bayan cika mako daya da fara rajistar masu kada kuri'a.
INEC ta lissafa jihohin Najeriya da suka fi yawan masu yankan katin zabe, inda aka bayyana Osun ta farko a Kudu, Kaduna kuma a Arewa.
Hukumar ta bayyana cewa za a cigaba da rajistar katin daga yanzu har zuwa Agustan 2026, sai dai ta yi kira da a yi rajistar da wuri.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

