Tinubu: Bayan an Yi Mata Ca, PDP Ta Faɗi Dalilin Tura Takarar Shugaban Ƙasa ga Kudu
- Jam’iyyar PDP ta ce matsayar da ta ɗauka na bai wa Kudu tikitin shugaban ƙasa a 2027 ra'ayin kanta ne
- Ta bayyana haka ne a lokacin da ƴan adawa ke zargin an ɗauki matakin domin dadaɗawa Ministan Abuja, Nyesom Wike
- Kakakin jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba, ya ce PDP ba ta taɓa kwantawa ba kamar yadda ƴan adawa ke faɗi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – PDP ta karyata ikirarin cewa zartar da tsarin bai wa Kudu tikitin shugabancin ƙasa a 2027 manufar jam'iyya mai mulki ce.
Jam’iyyar ta kuma bayyana cewa ba ta dauki matakin saboda ta faranta wa Ministan Abuja, Nyesom Wike ba.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Kakakin jam’iyyar na ƙasa, Hon. Debo Ologunagba, ne ya bayyana haka a afiyar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jam'iyyar PDP ta fara shirin babban taro
Daily Post t ruwaito cewa Hon. Debo Ologunagba, ya koro bayani a kan halin da PDP ke ciki da shirye-shiryen taro na ƙasa mai zuwa.
Ya ce PDP ba ta taɓa zama a kwantawa ba kamar yadda tsohon gwamnan Binuwai, Sanata Gabriel Suswan, ya yi zargi.
A cewarsa, PDP ta riga ta sake daidaita kanta don fuskantar 2027, kuma babu wani mutum guda da ya fi jam’iyyar.
Ya ce:
“Babu wani mutum ɗaya da aka ɗaukaka. Idan akwai wanda aka ɗaukaka, to PDP ce gaba ɗaya. Bayan zaɓen 2023 mun nazarci ayyukanmu, mun gano gibin da ke ciki, muka yi gyare-gyare, shi ya sa yanzu ake ganin haɗin kai PDP.'
2027: Jam'iyyar PDP ta kare matsayarta
Kakakin ya kara da cewa matakin bai wa Kudu tikitin shugabancin ƙasa na cikin ka’idojin PDP na karɓa-karɓan mulki tsakanin Arewa da Kudu.

Source: Facebook
Ologunagba ya ce:
“Bayan shawarwari, NEC ta amince a bar mukamai na Arewa a inda suke, a bar na Kudu a inda suke, sannan a bai wa Kudu kujerar Shugaban Kasa. Wannan ba don ɗaukaka mutum ɗaya ba ne, sai don adalci da haɗin kai.
Ologunagba ya ce koda yake akwai masu adawa daga ciki, irin su Sanata Abba Moro, jam’iyyar tana ci gaba da shawarwari don a yi sulhun.
Ya ce:
“Kyawun dimokuraɗiyya shi ne mutane na iya samun sabani. Amma abin da ya fi muhimmanci shi ne jam’iyya ta dawo da kowa kan teburin tattaunawa."
Ya kuma ce duk da an fi maida hankali ga sulhu, yanzu lokaci ya yi da za a fara ɗaukar matakin ladabtarwa kan waɗanda suka yi wa jam’iyya zagon ƙasa a 2023.
Ologunagba ya ƙaryata ikirarin Wike cewa ba a gayyace shi zuwa taron NEC ba, yana mai cewa an aiko da wasiƙa ofishinsa, an kuma wallafa sanarwa a jaridu.
Ya kuma ce PDP ta kammala shirye-shirye domin babban taronta na kasa da za a gudanar a Ibadan ranar 15 zuwa 16 ga Nuwamba, 2025.
PDP ta magantu kan kinkimo Jonathan
A baya, mun wallafa cewa bayanai suna kara fitowa kan alakar jam’iyyar PDP da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, domin tsaya mata takarar Shugaban Ƙasa.
Bayanan na fito wa bayan jam'iyyar ta amince da fito dan takarar Shugaban Najeriya daga Kudancin kasar nan a kakar babban zaben 2027 mai zuwa.
Mai magana da yawun jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba, ne ya mayar da martani kan jita-jitar takarar shugaban kasa da ake alakantawa da Jonathan.
Asali: Legit.ng


