"Ka Ankara": Kungiya Ta Fallasa Makarkashiyar da Ake Kullawa Jonathan kan 2027
- Batun maido tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, zuwa fagen siyasa na ci gaba da daukar hankali a Najeriya
- Kungiyoyi da dama sun fito sun yi kira ga Jonathan da ya fito takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027
- Sai dai, wata kungiya daga yankin Niger Delta, na ganin wani tarko ne ake hadawa tsohon shugaban kasan na Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Rivers - Kungiyar South-South Reawakening Group (SSRG), ta shawarci tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, kan yin takara a 2027.
Kungiyar SSRG ta shawarci Jonathan da ya yi hattara da kungiyoyi daban-daban da ke kiransa ya tsaya takarar shugabancin kasa a zaɓen 2027.

Source: Facebook
Shugaban kungiyar, Dr. Joseph Ambakaderimo, ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wace kullalliya ake shiryawa Jonathan a 2027?
Dr. Joseph Ambakaderimo ya ce duk wani yunkuri na Jonathan na amincewa da irin wannan kira, zai kai shi ga zuwa karshen tasirinsa a siyasance.

Kara karanta wannan
Bayan kai tikitin takarar PDP Kudu, Sanata ya fadi shirin jam'iyyar kan Jonathan da Peter Obi
Shugaban na kungiyar SSRG ya bayyana cewa waɗanda ke yi masa wannan kira, ba kyakkyawar niyya suke da ita a gare shi da Najeriya ba.
Dr. Joseph Ambakaderimo ya bayyana cewa kungiyoyi kusan guda shida daga yankin Niger Delta sun gana kwanan nan domin nazarin tasirin kiraye-kirayen da wasu daga Arewa ke yi na jawo Jonathan cikin siyasa.
Ya ce sun cimma matsayar cewa waɗanda ke bayan wannan shiri abokan gaba ne na Najeriya.
An soki masu neman Jonathan ya yi takara
"Ku koma tarihi, za ku ga cewa waɗannan su ne mutanen da suka tsani Jonathan lokacin yana shugaban kasa. Sun ce ba shi da karfi, ba ya iya kare Najeriya daga ta’addancin Boko Haram. To, me ya sauya yanzu haka?"
"Ba mu ga wani bayani daga Jonathan kan wannan labari na shigar da shi takara a 2027 ba. Don haka bana son yin magana mai yawa sai dai idan shi Jonathan ya fito ya bayyana niyyarsa.”
"Ta yaya ne kwatsam waɗanda suka yi aiki domin ganin bayan Jonathan, suka yi masa mummunar magana kala-kala, yanzu su ne ke nuna soyayya da kauna gareshi suna kuma kiransa ya farfado daga barcin da ya yi a siyasa?
"Fahimtata ita ce akwai babban shiri na tarwatsa kuri’un Kudu ta hanyar fitowa da ‘yan takara da yawa daga Kudu domin su raba kuri’un, yayin da za a bar kuri’un Arewa wuri guda, ta hanyar fito da sanannen ɗan takara."
- Dr. Joseph Ambakaderimo

Source: Facebook
Batun takarar Jonathan a 2027 na kara girma
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Mathias Tsado, na son Goodluck Jonathan ya yi takara a zaben shekarar 2027.
Mathias Tsado ya bukaci makusantan Jonathan da ba su ba shi shawara don ya sake jaraba sa'arsa wajen neman shugabancin Najeriya.
Tsohon dan takarar ya bayyana cewa dawowar Jonathan kan madafun ikon kasar nan, zai sanya a shawo kan matsalolin tattalin arziki da tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
