Gwamna Ya Samu Gagarumin Goyon Baya, Ana So Ya Nemi Takarar Shugaban Kasa a 2027
- Jam'iyyar PDP na ci gaba da kokarin lalubo dan takarar da zai iya kayar da APC a babban zaben shugaban kasa na 2027
- Wani jigo a jihar Oyo ya bayyana cewa Gwamna Seyi Makinde na da duk abin da ake bukata na kawo sauyi mai amfani a Najeriya
- Femi Babalola ya caccaki gwamnatin APC mai ci, yana mai cewa ta gaza cika allawurran da ta daukar wa yan Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Oyo - Bayan PDP ta ware tikitin takarar shugaban kasa ga Kudancin Najeriya, an fara nuna wadanda suka dace jam'iyyar ta yi nazari a kansu.
Wani jigon PDP a jihar Oyo ya bayyana Gwamna Seyi Makinde a matsayin wanda ya fi cancanta ya kare martabar PDP a babban zaben 2027.

Source: Facebook
Jigon jam’iyyar, Femi Babalola, ya bayyana hakan a wata hira da Tribune Online a Ibadan ranar Talata, 26 ga watan Agusta, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Makinde ya samu goyon baya
Femi Babalola ya ce Makinde na da duk abin da ake bukata don gyara kura-kuran da ake gani a kasa, duba da irin nasarorin da ya samu a duka fannoni a matsayinsa na gwamnan jihar Oyo.
Ya ce gwamnatin jam’iyyar APC a matakin kasa ta gaza cika alkawurran da ta daukar wa yan Najeriya, don haka lokaci ya yi da za canza.
“APC ta shahara wajen alkawuran karya da na bogi, babu abin da ta iya tabukawa face kawo yunwa da talauci, wadanda suka addabi jihohin Najeriya," in ji shi.
Ana son gwamna Makinde ya nemi takara
Babalola ya ce a halin matsin da kasar nan ke ciki, tana bukatar mutum mai sababbin dabaru da tunani, wadanda za su iya kawo sauyi a rayuwar jama'a.
A cewarsa, Gwamna Makinde na daya daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa masu tasiri wanda ya cancanci rike mulkin Najeriya

Kara karanta wannan
Kudin fansa: 'Yan bindiga sun dauke mutum 4700, an ji biliyoyin da aka rasa a shekara 1
Babalola ya bayyana cewa Gwamna Makinde zai iya fafatawa da manyan ‘yan takara irin su Peter Obi, kuma ya iya zama dan takarar jam’iyyar PDP a zaben 2027.
“Gwamna Makinde ya yi aiki mai kyau, ko da kuwa an samu kura-kurai, dama ba zai yiwu ya zama 100 bisa 100 ba, amma idan aka kwatanta shi da gwamnonin baya, ya shiga gaba,” in ji shi.
Femi Babalola zai iya fitowa takara a Oyo
Da yake magana kan yiwuwar shi ma ya tsaya takarar gwamnan jihar Oyo a 2027, Babalola ya ce:
“Ina bibiyar wadanda suka nuna sha'awa, idan ban gamsu da irin wadanda suka fito ba, zan iya tsayawa takara a 2027.
“Kodayake ba shi ne babban burina ba yanzu, amma ina ganin Oyo na bukatar gwamna mai zurfin sanin jihar bayan wa’adin Makinde.
“Ba zan goyi bayan ‘yan takara masu amfani da tsarin jam’iyya don amfanin kansu ba, zan fi goyon bayan masu adalci da amfanar jam’iyya.
- Femi Babalola.

Source: Facebook
PDP ta yi kuskuren tsaida Atiku a 2023
A wani labarin, kun ji cewa shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Abba Moro ya ce PDP ta yi kuskure da tsaida Atiku Abubakar takara a 2023.
Sanata Abba Moro ya ce PDP ta yi nadamar tsaida Atiku kuma ba za ta bari ta sake maimaita irin wannan kuskuren ba a zabuka masu zuwa.
Ya kuma yabwa kwamitin zartarwa na PDP ta kasa, wanda ya mika tikitin takarar shugaban kasa ga kudancin Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

