Rigimar Shugabanci a ADC Ta Gawurta, Yankin Atiku Sun Jawo Rikici Ya Dawo Danye

Rigimar Shugabanci a ADC Ta Gawurta, Yankin Atiku Sun Jawo Rikici Ya Dawo Danye

  • Matsalar da ta tunkaro gamayyar ƴan adawa a ADC ya sake salo duk da ta yi gaggawar daukar mataki
  • ADC ta reshen Arewa maso gabas ta jam’iyyar ADC ta bayyana goyon bayanta ga Hon. Nafiu Bala a matsayin shugaban jam'iyya
  • Shugabannin yankin sun ce sanarwar korar Nafi'u da wani Auwal Barde ya fitar ba ta wuce takardar kawai ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Gombe – Rigimar shugabanci da ta dabaibaye jam’iyyar ADC ta ci gaba da ɗaukar sabon salo duk da sanar da korar Nafi'u Bala da ake zargin ya ɗauko rigimar.

Shugabannin yankin Arewa maso Gabas na jam’iyyar sun hada baki wajen bayyana goyon bayansu ga Hon. Nafiu Bala a matsayin mukaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa.

Kara karanta wannan

Ina makomar Tinubu?: APC ta ce za ta ba kowa dama ya tsaya takarar shugaban ƙasa

Wasu jagororin ADC sun nuna Shugabansu
H-D: Nafi'u Bala, Jagororin ADC a taron bayyana jam'iyya Hoto: Nafiu Bala/Atiku Abubakar
Source: Facebook

Nigerian Tribune ta wallafa cewa bayanin hakan ya fito ne daga taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a Bauchi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan ADC suna adawa da jagorancin David

Jaridar Leaderhip ta wallafa cewa Shugabannin kungiyar ADC daga jihohi shida na yankin sun halarci wani taro da aka gudanar a Bauchi inda su ka nuna rashin goyon bayan David Mark.

A cikin sanarwar da aka karanta daga bakin Hon. Shehu Usman, sakataren yada labarai na yankin, ya ce:

"Mun yarda da murabus ɗin Cif Ralph Okey Nwosu ya yi daga shugabancin jam'iyyar na ƙasa, tare da amincewa da miƙa jagorancin ADC ga Hon. Nafiu Bala a matsayin mukaddashin Shugaba.”
Nafi'u Bala ya kara samun goyon baya
Nafi'u Bala a taron manema labarai Hoto: Nafiu Bala
Source: Facebook

Sun ƙara da tabbatar da biyayyarsu ga sabon shugaban domin tabbatar da ci gaba da daidaito a jam’iyyar.

Ƴan ADC sun yi watsi da korar Nafi'u

Kungiyar ta bayyana cewa sanarwar da wani Auwal Barde ya yi na Nafiu Bala, ba ta da inganci.

Kara karanta wannan

Tura ta kai bango: 'Yan majalisar PDP sun taso Tinubu a gaba kan tsadar rayuwa

Sun ce Barde ba shugaban jam’iyyar ADC na Gombe ba ne, don haka ba shi da wata dama ta fitar da irin wannan sanarwa.

Haka kuma, sun bayyana cewa babu wani lokaci da aka zargi Nafiu Bala da rashin ladabi ko karya tsarin jam’iyyar, kundin tsarin mulki na ƙasa ko dokar zabe. Jagororin sun bayyana cewa, a ranar 25 ga Agusta, 2025, Nafi'u ya ziyarci mazabarsa ta Nassarawo, Gombe.

Shugabannin sun tabbatar da cewa an tarbe shi da farin ciki daga shugabanni da magoya baya ba tare da maganar kora ba.

Sun yi kira ga dukkanin ƴan ADC da magoya baya da su haɗu domin gina Najeriyar da kowa zai mora.

Jam'iyyar ADC ta taso APC a gaba

A baya, mun wallafa cewa jam’iyyar ADC ta zargi APC mai mulki da amfani da hukumar EFCC a matsayin makami don tsoratar da ‘yan siyasar adawa a kasar nan.

A wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Malam Bolaji Abdullahi, ya fitar ta yi gargadin cewa hakan zai iya lalata amincewar da jama’a su ka yi da EFCC.

Jam’iyyar ta ce, wasu matakan baya-bayan nan na hukumar, daga ciki har da dawo da tsofaffin shari’o’i da kuma gayyatar ƴan adawa, na nuna alamar siyasa a ciki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng