"An Makara": Hadimin Wike Ya Hango Kuskure a Matakin PDP Na Kai Tikitin Takara Kudu

"An Makara": Hadimin Wike Ya Hango Kuskure a Matakin PDP Na Kai Tikitin Takara Kudu

  • Ana ci gaba da yin muhawara kan matakin da PDP ta dauka na kai tikitin takarar shugaban kasa na zaben 2027 zuwa yankin Kudu
  • Hadimin ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, na ganin cewa wannan matakin an makara wajen daukarsa
  • Lere Olayinka ya bayyana cewa ba yanzu bane lokacin da ya kamata jam'iyyar hamayyar ta kai tikitin nata zuwa Kudu ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mai magana da yawun ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, Lere Olayinka, ya yi magana kan kai tikitin takarar shugaban kasa na PDP zuwa yankin Kudu.

Lere Olayinka ya bayyana cewa shawarar jam’iyyar PDP, na kai tikitin shugabancin kasa na 2027 zuwa yankin Kudu, ya zo a makare.

Hadimin Wike ya caccaki jam'iyyar PDP
Hoton shugaban PDP na kasa, Umar Damagum da ministan Abuja, Nyesom Wike Hoto: @OfficialPDPNig, @GovWike
Source: Facebook

Hadimin na Wike ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin 'Politics Today' na tashar Channels Tv a ranar Laraba, 27 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan

Dele Momodu: 'Yadda Wike da Tinubu su ka kawo tsarin miƙa mulki Kudu a PDP'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin Wike ya fadi kuskuren PDP

Lere Olayinka ya bayyana cewa, da jam’iyyar ta saurari Wike da sauran mambobin da suka fusata kafin zaɓen 2023, da PDP ba za ta shiga cikin rikici ba.

"An makara domin mun samu damar yin abin da ya dace shekaru uku da suka gabata amma ba mu yi ba."
"Idan da mun yarda da shi (Wike), da watakila jam’iyyar ba ta kasance inda take a yau ba. Kai ya riga ya yanke, yanzu muna kuka. Abin da ya kamata mu yi shekaru uku da suka wuce, ba mu yi ba."
Lere Olayinka ya tuna cewa a shekarar 2022, Wike da abokan siyasarsa na G-5 sun nemi a bai wa Kudu tikitin shugabancin kasa.
Ya ce a lokacin sun bayyana cewa adalci ya wajabta hakan, ganin cewa tsohon Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya fito daga Arewa ke kammala wa’adinsa.
Hadimin na Wike ya bayyana cewa PDP yanzu tana fuskantar ƙalubale mai girma a siyasa gabanin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

"Mun yi nadama": Sanata ya fadi kuskuren PDP kan Atiku a zaben 2023

"Abu na biyu da ya sa aka makara shi ne yanzu kuna cewa shugaban kasa ya fito daga Kudu, amma matsalar ita ce jam’iyya mai mulki tana da ɗan takara daga Kudu kuma wannan ɗan takara zai shafe shekara huɗu a ofis, ya rage masa sauran shekaru huɗu."
"Yanzu kun gabatar da ɗan takararku (na Kudu) ga Arewa, shin Arewa za ta yarda da ɗan takarar da zai fara daga farko? Wani ɗan takara da watakila zai nemi wa’adi na biyu idan ya ci a 2031? Ko kuwa ɗan takarar da zai yi shekaru huɗu kaɗai?"

- Lere Olayinka

Hadimin Wike ya caccaki PDP
Hoton ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, yana jawabi a wajen taro Hoto: @GovWike
Source: Facebook

Jam'iyyar PDP ta kai tikitin takara Kudu

A baya-bayan dai PDP ta yanke shawarar kai tikitin shugabancin kasa na 2027 zuwa Kudu, matakin da mutane irin su Lere Olayinka suka bayyana a matsayin wanda ba zai haifar da sakamakon da ake fata ba.

A halin da ake ciki kuma, domin magance damuwar da ta shafi Arewa na samun ɗan takarar da zai yi shekaru huɗu kacal, ana rade-radin cewa PDP na zawarcin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da Peter Obi.

Moro ya ce PDP ta yi kuskure a 2023

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Abba Moro, ya bayyana cewa PDP ta yi kuskure a zaben 2023.

Kara karanta wannan

'APC da PDP sun tafka kuskure, da yiwuwar su sha kaye a zaben shugaban kasa na 2027'

Sanata Abba Moro ya bayyana cewa tsayar da Atiku Abubakar takara a 2023, kuskure ne babba wanda ya jawo rashin nasara ga jam'iyyar.

Hakazalika, ya nuna cewa jam'iyyar ta yi nadamar daukar wannan matakin domin ya jawo mata mummunar rashin nasara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng