"Mun Yi Nadama": Sanata Ya Fadi Kuskuren PDP kan Atiku a Zaben 2023

"Mun Yi Nadama": Sanata Ya Fadi Kuskuren PDP kan Atiku a Zaben 2023

  • Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Abba Moro, ya tuna baya kan abubuwan da suka faru a lokacin zaben shekarar 2023
  • Sanata Abba Moro ya bayyana cewa tsayar da Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa na PDP, babban kuskure ne
  • Ya nuna cewa wannan kuskuren na daga cikin dalilan da suka jawo jam'iyyar PDP ta kwashi kashinta a hannu a wajen APC a zaben 2023

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Wani jigo na PDP, Sanata Abba Moro, ya yi magana kan kuskuren da jam'iyyar ta yi a kan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Sanata Abba Moro wanda shi ne shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, ya ce PDP ta yi nadamar tsayar da Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban kasa a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Bayan kai tikitin takarar PDP Kudu, Sanata ya fadi shirin jam'iyyar kan Jonathan da Peter Obi

Sanata Abba Moro ya yi magana kan Atiku
Hoton tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Abba Moro Hoto: Atiku Abubakar, Comrade Abba Moro
Source: Facebook

Sanata Abba Moro ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana tsayar da Atiku a matsayin kuskure da ya jefa jam’iyyar cikin asara mai girma.

Sanata Abba Moro ya yabi PDP-NEC

Sanata Abba Moro, ya bayyana cewa kwamitin zartarwa na kasa (NEC) na jam’iyyar ya ɗauki mataki mai kyau wajen kai tikitin takarar shugaban ƙasa na 2027 zuwa yankin Kudu.

Ya ce matakin kai tikitin zuwa Kudu, an gina shi bisa adalci, daidaito, da gaskiya.

"Kai tikitin zuwa Kudu gyara ne na manyan kura-kurai da aka tafka a baya. Ga waɗanda suke da shakku kan juriyar PDP, hakan tabbas abin mamaki ne."
"Za ku tuna na taɓa gaya muku cewa PDP ta ɗauki matakai da dama domin shawo kan rikice-rikicen cikin gida. Kuma daga cikin tozarci da rikici, za mu sake farfadowa da karfinmu."

Kara karanta wannan

PDP ta koka, ta zargi EFCC da garkame manyan 'ya 'yanta 2 a Kaduna

- Sanata Abba Moro

Wane kuskure PDP ta yi kan Atiku?

Yayin da yake tsokaci kan zaɓen 2023, Sanata Abba Moro ya amince cewa tsayar da ɗan takara daga Arewa irin Atiku babban kuskure ne.

Sanata Abba Moro ya fadi kuskuren PDP a 2023
Hoton Sanata Abba Moro a zauren majalisar dattawa Hoto: Comrade Abba Moro
Source: Facebook
"Yawancinmu, kusan dukkanmu, mun amince cewa kuskure ne a 2023 tsayar da ɗan takara daga Arewa."
“Amma a wannan karon, a cikin yanayin haɗin kai, da adalci da gaskiya, shugabannin PDP sun yanke shawarar ɗaukar mataki mai wahala suka ce, bari mu mayar da wannan abu Kudu, inda mafi yawan ‘yan Najeriya suka zata ya kamata a kai tun farko.”

- Sanata Abba Moro

Shugaban marasa rinjayen na majalisar dattawa ya tabbatar da cewa jam’iyyar na nadamar sakamakon zaben 2023.

"Rasa babban zaɓe mai tarihi a irin wannan mummunan yanayi tabbas abu ne na nadama.”

- Sanata Abba Moro

Atiku Abubakar zai yi takara a 2027?

A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar ya bayyana aniyarsa ta sake yin takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya hango kuskuren PDP, ya faɗi yadda hakan zai taimaki Tinubu a 2027

Atiku ya musanta wasu rahotanni da ke cewa yana shirin janyewa daga yin takarar shugaban kasa, ya ce zai jarraba sa'arsa.

Tsohon mataimakin shugaban kasan ya nuna cewa duk mai kishin Najeriya, dole ne ya zo a hada hannu da shi don kawar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng