Surutu Ya Kare, PDP Bayyana Yankin da Za Ta Dauko Dan Takarar Shugaban Kasa a 2027

Surutu Ya Kare, PDP Bayyana Yankin da Za Ta Dauko Dan Takarar Shugaban Kasa a 2027

  • A yau Litinin, 25 ga watan Agusta, 2025 jam'iyyar PDP ta gudanar da taron Kwamitin Zartarwa (NEC) a birnin tarayya Abuja
  • A taron, shugabannin PDP sun warware wasu daga cikin batutun da ake ta ce-ce-ku-ce a kansu ciki har da batun tikitin takarar shugaban kasa
  • Jam'iyyar ta amince da bi wa Kudancin Najeriya takarar shugaban kasa a zaben 2027 tare da tabbatar da kujerar shugaban PDP ga Arewa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawonshekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Kwamitin Zartarwa (NEC) na jam’iyyar PDP ta kasa ya amince da ware tikitin takarar shugabancin kasa na zaben 2027 ga yankin Kudancin Najeriya.

Shugabannin babbar jam’iyyar adawar sun yanke wannan hukunci ne yayin taron NEC da aka gudanar a Abuja a ranar Litinin, 25 ga watan Agusta, 2025.

Taron PDP ta kasa.
Hoton shugabannin PDP a taron NEC da ya gudana a Abuja ranar Litinin, 25 ga watan Agusta, 2025 Hoto: @officialPDPNig
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da PDP ta wallafa a shafinta na X jim kadan bayan kammala taron NEC, majalisar koli da ke yanke hukunci a jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Umar Damagum: PDP ta dauki mataki kan kujerar shugabanta na kasa

A cikin sanarwar, mai magana da yawun jam'iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya bayyana cewa NEC ta amince da shawarwarin kwamitin raba mukamai bayan dogon tattaunawa.

Yadda jam'iyyar PDP ta raba mukaman shugabanninta

Ya ce tsarin raba mukaman kwamitin zartarwa na kasa (NWC) na yanzu zai ci gaba da aiki har zuwa babban taron jam’iyya na watan Nuwamba, inda za a zabi sabbin shugabanni.

Sanarwar ta ce:

"Duk mukaman jam’iyyar PDP na kasa da ke Arewacin Najeriya za su ci gaba da kasancewa a yankin, haka nan duka mukaman jam’iyyar da ke Kudancin Najeriya za su ci gaba da zama a yankin.
"Tunda an bar wa Arewa kujerar shugaban jam’iyya PDP na kasa, dan takarar shugabancin kasa na PDP a zaben 2027 zai fito ne daga Kudancin Najeriya.
“Bayan haka kuma an umurci kowanne yanki ya fara tsara yadda zai raba mukamai a cikinsa domin aiwatar da wannan mataki yadda ya kamata.”

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Fitacciyar 'yar wasan barkwanci ta rasu a 'taron matar gwamna' a Najeriya

NEC ta gamsu da shirye-shiryen babban taron PDP

NEC ta bayyana gamsuwa da shirye-shiryen jam’iyyar a rassan jihohi da sauran tsare-tsaren da PDP ke yi domin babban taronta na kasa da za a gudanar a Ibadan, jihar Oyo, a ranakun 15 da 16 ga watan Nuwamba, 2025.

Haka kuma, NEC ta karbi rahoton kwamitin gyaran kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP, cewar rahoton The Cable.

Ta umarci kwamitin da ya raba kwafin sababbin dokokin da aka yi wa gyara zuwa ga rassan jam’iyya da sauran bangarori domin samun karin shawarwari.

Damagum zai cigaba da rike PDP

Bayanai sun zo bayan taron NEC da jam'iyyar PDP ta gudanar cewa Ambasada Umar Iliya Damagum ya samu karin girma a majalisar NWC.

PDP ta tabbatar da shi a matsayin shugabanta na kasa. Majalisar kolin jam'iyyar hamayyar ta bayyana iyakar lokacin da zai rike wannan mukamin.

PDP ta yanke shawarar cewa Damagum, wanda ya shafe sama da shekara guda yana rike da mukamin shugaban rikon kwarya, a ɗaga shi zuwa cikakken shugaban jam’iyyar na kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262