'Yan Majalisa 3 Sun Fice daga NNPP, APGA, Sun Sauya Jam'iyya a Najeriya
- Jam'iyyar NNPP ta rasa yan Majalisa biyu da take da su a zauren Majalisar dokokin jihar Taraba da ke Arewa maso Gabas
- Mambobi uku daga NNPP da APGA sun tabbatar da sauya sheka zuwa PDP mai mulkin jihar Taraba a hukumance yau Litinin
- Kakakin Majalisa ya bayyana cewa wannan na kara nuna kokarin da Gwamna Agbu Kefas ke yi na kawo sauyi a rayuwar al'ummar Taraba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Taraba - Yan Majalisar Dokokin jihar Taraba guda uku sun fice daga jam'iyyun adawa, sun sauya sheka zuwa PDP mai mulki.
Mambobi uku na jam’iyyun adawa a Majalisar Dokokin Taraba sun tabbatar da hakan ne a zamansu na yau Litinin, 25 ga watan Agusta, 2025.

Source: Facebook
Channels tv ta rahoto cewa biyu daga cikin yan majalisa sun fito ne daga NNPP yayin da daya kuma ya baro APGA, dukansu sun koma PDP mai mulkin jihar a hukumance.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan Majalisa 3 sun fita daga NNPP, APGA
Yan Majalisar sun hada da Hon. Umar Adamu, mai wakiltar mazabar Jalingo 1 wanda ya fito daga jam’iyyar NNPP, da Hon. Zakari Sanusi, mai wakiltar mazabar Ibi, wanda shi ma ya fito daga NNPP.
Na uku kuwa shi ne Hon. Anas Shaibu, dan majalisa mai wakiltar mazabar Karim 2, wanda ya sauya sheka daga jam’iyyar APGA.
Kakakin majalisar Dokokin jihar Taraba, Hon. John Kizito, ya tabbatar da hakan a wasikun sauya shekar da mambobin suka rubuta a zamansu na yau Litinin.
Bayan karanta wasikun, kakakin Majalisar ya bayyana cewa wannan sauya sheka ta kara nuna kokarin da Gwamna Agbu Kefas na kawo ci gaban jihar Taraba.
Hon Kizito ya kara da cewa mambobin sun yi dogon nazari da tuntuba tare da masu ruwa da tsaki, abokan siyasa da al’ummar mazabunsu kafin daukar matakin.
Dalilin yan Majalisar na komawa PDP
A wasikar sauya shekarsa, Hon. Anas Shaibu ya bayyana cewa shiga PDP za ta ba shi damar yin aiki mafi inganci wajen kare muradun al’ummar mazabarsa, tare da bada gudummawa ga ci gaban jihar Taraba.
Haka zalika, Umar Adamu ya ce:
“Na gode da damar da na samu a NNPP, amma bayan dogon nazari da tattaunawa da mutanen Jalingo 1, na ga manufofin PDP sun fi dacewa da burinmu.”
Hon. Zakari Sanusi, wanda ke wakiltar Ibi, ya maimaita irin wannan bayani a wasikar sauya shekar da ya mika wa Majalisa.

Source: Facebook
A halin yanzu, daga cikin mambobi 23 na Majalisar Dokokin Jihar Taraba, PDP na da mambobi 16, yayin da jam'iyyar APC ke da takwas, rahoton Daily Post.
PDP ta nemi a kwace kujerun 'yan Majalisa 4
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta maka yan Majalisar Tarayya hudu a gaban kotu, ta nemi a kwace kujerunsu saboda sun sauya sheka zuwa APC.
A cewar PDP, abin da yan majalisar suka yi ya sabawa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima.
Rahoto ya nuna cewa wadanda PDP ta maka a kotun da ke Abuja sun hada da sanatoci biyu da yan Majalisar Wakilan Tarayya guda biyu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

