"Rashin Tausayi": Jam'iyyar ADC Ta Caccaki Gwamnonin PDP, Ta Fadi Kuskuren da Suka Yi

"Rashin Tausayi": Jam'iyyar ADC Ta Caccaki Gwamnonin PDP, Ta Fadi Kuskuren da Suka Yi

  • Jam'iyyar ADC ta fito ta ragargaji gwamnonin PDP mai adawa a Najeriya bayan sun hadu sun gudanar da taron siyasa a jihar Zamfara
  • Mukaddashin sakataren yada labarai na kasa na ADC, ya bayyana cewa matakin da gwamnonin suka dauka na yin taro a Zamfara bai dace ba
  • Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa gwamnonin sun nuna rashin tausayi ta hanyar kin la'akari da halin da Zamfara take ciki na zubar da jinin bayin Allah

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar hadaka watau ADC ta soki gwamnonin PDP kan gudanar da taron siyasa a jihar Zamfara.

Jam'iyyar ADC ta ce yin taron kwanaki kaɗan bayan an kashe mutane da dama a jihar, ko kadan bai dace ba.

Jam'iyyar ADC ta soki gwamnonin PDP
Hoton gwamnonin PDP bayan sun kammala taro a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mukaddashin kakakin jam'iyyar ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar a ranar Lahadi a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

'Ka dawo gida da gaggawa: An buƙaci Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci a jihohin Arewa 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Cable ta ce an sace mutane 144, an kashe 24, sannan 16 sun jikkata a kananan hukumomi daban-daban na jihar a cikin 'yan kwanakin nan.

Gwamnonin na PDP sun gudanar da taronsu a jihar Zamfara a ranar Asabar, 23 ga watan Agustan 2025.

Me ADC ta ce kan taron gwamnonin PDP?

ADC ta bayyana taro a matsayin “rashin tausayi” da kuma nuna wulakanci ga mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren.

"Maimakon gwamnonin su tattaru su goyi bayan takwaransu wanda yake cikin mawuyacin hali, domin a nemo mafita ga wannan mummunan kisan gilla, sai suka zaɓi gudanar da gangamin siyasa a wurin da aka yi kisan gilla, koda hakan na nufin take mutuncin waɗanda suka mutu."
"Hotunan gwamnonin PDP sanye da kayayyakin alfarma suna murmushi ga kyamara, tamkar ba a cikin wurin da ke cike da jini da bakin ciki suke ba, abu ne da bai dace ba."

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun cimma matsaya 1, sun kalubalanci Wike

"Wannan aikin shi kaɗai ya sake tabbatar da muhimmiyar gaskiya guda ɗaya, jam’iyyar APC da PDP da ba za ta taɓa gyaruwa ba, ba su damu da rayuwar jama’a da wahalarsu ba. Abin da suka damu da shi kawai shi ne mulki da siyasa."

- Bolaji Abdullahi

Jam'iyyar ADC ta caccaki Bola Tinubu

Haka kuma, ADC ta kuma soki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan yawaitar kashe-kashe a jihohin Zamfara da Katsina.

ADC ta soki Shugaba Tinubu
Hoton mukaddashin kakakin ADC na kasa, Bolaji Abdullahi Hoto: @BolajiADC
Source: Facebook

Ta bukaci shugaban kasan da ya dawo gida Najeriya domin fuskantar matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.

Jam'iyyar ADC ta kuma nemi da ya sanya dokar ta baci a jihohin Zamfara da Katsina don shawo kan hare-haren 'yan bindiga.

Gwamnonin PDP sun kalubalanci Wike

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnonin jam'iyyar PDP sun kalubalanci ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Gwamnonin sun cimma matsayar amincewa da matakin da kwamitin NEC ya dauka na gudanar da babban taron jam'iyyar na kasa.

Sun bayyana cewa ba za su amince wani ya kawo cikas ga babban taron na jam'iyyar ba don cimma wasu bukatu na kashin kansa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng