Gwamnonin PDP Sun Cimma Matsaya 1, Sun Kalubalanci Wike

Gwamnonin PDP Sun Cimma Matsaya 1, Sun Kalubalanci Wike

  • Gwamnonin jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya sun gudanar da babban taro a birnin Gusau na jihar Zamfara
  • Sun cimma matsaya kan amincewa da matakin da kwamitin NEC ya dauki dangane da gudanar da babban taron jam'iyyar
  • Gwamnonin sun aika da sakon gargadi kan duk masu son kawo cikas ga bababn taron da jam'iyyar ta shirya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Kungiyar gwamnonin PDP a ranar Asabar ta aika da sakon gargadi ga ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, da sauran masu son kawo cikas ga jam'iyyar.

Gwamnonin na PDP sun gargadi Wike da ire-irensa da su guji kawo cikas ga babban taron jam’iyyar na kasa da aka shirya gudanarwa a Ibadan, jihar Oyo, a ranar 15 ga Nuwamba, 2025.

Gwamnonin PDP sun yi taro a Zamfara
Hoton gwamnonin PDP bayan kammala taro a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa bayan kammala taronsu na bakwai da aka gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Agusta, 2025 a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

'Karshen APC ya zo,' Gwamnonin PDP sun faɗi abin zai hana jam'iyya mai mulki sake cin zaɓe

Wike na adawa da matakin PDP

Wike dai ya bayyana rashin jin daɗinsa game da kwamitin rikon kwarya na Kudu maso Kudu, tare da adawa da ci gaba da rike Ali Odefa a matsayin mataimakin shugaban jam’iyya na kasa (Kudu maso Gabas).

Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya yi gargaɗin cewa sabon rikici na iya tasowa idan PDP ta ki amincewa da zaben shugabannin Kudu maso Kudu, inda aka zabi abokinsa, Dan Orbih, a matsayin mataimakin shugaban jam’iyya na kasa (Kudu maso Kudu).

Gwamnonin PDP sun aika da gargadi

Gwamnonin sun sake jaddada cikakken goyon bayansu ga matsayar da Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC) na jam’iyyar ya cimma a taronsa na 101 da aka gudanar a watan Yulin 2025 dangane da babban taron jam’iyyar na 15 ga Nuwamba, 2025.

Gwamnonin sun bukaci mambobin jam’iyyar da su ƙi amincewa da duk wani yunƙuri da zai kawo tangarda ga babban taron, rahoton jaridar The Cable ya tabbatar.

Kara karanta wannan

2027: Gwamnonin PDP 8 sun tsayar da abin da suke yi, sun nufi jihar Zamfara

Sun kuma bayyana PDP a matsayin garkuwar dimokuraɗiyya ta hakika da kuma madogara ta gaskiya wacce za ta iya dawo da Najeriya kan tafarkin kyakkyawan shugabanci da ci gaban kasa.

Gwamnonin sun ja kunnen Wike
Hoton gwamnonin PDP bayan kammala wani taro Hoto: @seyimakinde
Source: Twitter
"Kungiyar gwamnonin PDP na sake tabbatar da cikakken goyon bayanta ga matsayar taron NEC na 101 da aka gudanar a watan Yulin 2025 dangane da babban taron jam’iyya na kasa da za a yi a ranar 15 ga Nuwamba, 2025."
"Muna kira ga mambobi su ki yarda da duk wani yunkuri daga masu adawa da jam’iyya da ke kokarin kawo tangarda ga taron."
"Su ci gaba da kallon PDP a matsayin ginshikin dimokuraɗiyya da kuma madafa ta gaskiya wajen farfaɗo da Najeriya a kan tafarkin kyakkyawan shugabanci da ci gaban kasa."

- Gwamnonin PDP

Wike ya fadi matsayarsa kan masu goyon bayan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa yana tare da masu goyon bayan Shugaba Bola Tinubu.

Ministan ya bayyana cewa yana tare da duk masu goyon bayamn shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Ya bayyana cewa baya la'akari da jam'iyyar mutum, idan har yana goyon bayan Tinubu, tabbas yana tare da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng