Kungiyar APC Ta Gargadi Tinubu kan Sauya Shettima, Ta Fadi Barazanar da Ke Tafe
- Kungiyar APC North Central Forum ta shiga sahun masu ba shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, shawara kan Kashim Shettima
- Shugaban kungiyar ya shawarci mai girma Bola Tinubu da ka da ya sauya Shettima don tsoron rasa kuri'un yankin Arewa ta Tsakiya
- Saleh Zazzaga ya nuna cewa ajiye Kashim Shettima na iya jawowa shugaban kasan matsala idan ya tashi neman tazarce a shekarar 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar APC North Central Forum ta ba shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, shawara kan Kashim Shettima.
Kungiyar ta bukaci Shugaba Tinubu kada ya sauya mataimakinsa, Kashim Shettima, a matsayin abokin takararsa kafin zaɓen 2027.

Source: Twitter
Wannan gargadin ya fito ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Alhaji Saleh Zazzaga, ya fitar a ranar Asabar a Abuja, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar ta yi gargadin cewa sauya Kashim Shettima na iya rage goyon bayan da Tinubu yake samu daga musulmin Arewa.
An bukaci Tinubu ya sauya Shettima
A kwanakin baya, wasu ’yan siyasa sun matsa wa Shugaba Tinubu lamba da ya sauya tikitin APC na Muslim-Muslim.
Sun yi nuni da cewa tikitin ya taka rawa wajen jawo wa jam’iyyar cikas a wasu jihohin Arewa a zaɓen 2023, ciki har da Nasarawa, Plateau, da kuma babban birnin tarayya, Abuja.
'Yan APC sun kare tikitin Muslim-Muslim
Sai dai a martanin da kungiyar ta yi, ta kare tikitin Muslim-Muslim, tana cewa wata dabara ce aka yi don zaben 2023, wadda ba ta tauye wakilcin addini ba, rahoton The Punch ya tabbatar.
Kungiyar ta jaddada cewa manyan Kiristoci daga yankin Arewa ta Tsakiya, suna rike da manyan mukamai a gwamnatin Tinubu, ciki har da shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda da kuma sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta ragargaji Atiku, El Rufa'i kan wata nasarar da Tinubu ya samu
"Tikitin Muslim–Muslim ba zai shafi damar Shugaba Tinubu a Arewa ta Tsakiya ba."
"Duba da manyan mukamai da Kiristocin Arewa ta Tsakiya suka samu, mun yi imanin cewa yankin zai ci gaba da mara masa baya."
"Ayyukan da shugaban kasa ya yi a ofis su ne za su yanke hukunci, ba tsarin addini ba. Babu bukatar sauya dabarar da ta yi nasara.”
- Alhaji Saleh Zazzaga

Source: Getty Images
Ƙungiyar ta kuma nuna damuwar cewa maye sauya mataimakin shugaban kasan, ba zai sanya kungiyoyin da ba su marawa APC baya a 2023 ba, su dawo goyon bayanta yanzu.
Ta jaddada cewa ya kamata a mayar da hankali kan ingantaccen mulki da haɗin kan ƙasa, ba wai rade-radin siyasa ba.
Malamin addini ya yi hasashe kan tazarcen Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa faston cocin The Lord Grace Provinces, Joel Atuma, ya yi hasashe kan tazarcen mai girma Bola Tinubua zaben 2023.
Malamin addinin ya bayyana cewa jam'iyyun adawa ba za su iya hana Tinubu zarcewa ba a 2027, domin ya fi karfinsu.
Sai dai, ya nuna cewa akwai wani sharadi guda daya da idan ya cika, shugaban kasan ba zai kai labari ba a zaben 2027.
Asali: Legit.ng
