2027: An Zaɓi Sule Lamiɗo domin Takara da Jonathan? Tsohon Gwamnan Ya Magantu

2027: An Zaɓi Sule Lamiɗo domin Takara da Jonathan? Tsohon Gwamnan Ya Magantu

  • Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya yi magana kan jita-jitar cewa Olusegun Obasanjo ya zabe shi zama mataimakin Goodluck Jonathan
  • Lamido ya ce bai taɓa jin wannan magana daga bakin Obasanjo ba, kuma ya bayyana shi a matsayin jagora da shugaban siyasa har yanzu
  • Ya ce Jonathan ne mafi cancanta ga PDP don kayar da Bola Tinubu, yana mai cewa kwarewarsa ta jagoranci ta bambanta shi da sauran ’yan takara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon gwamnan Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sule Lamido ya yi magana kan zaben 2027 da ke tafe.

Lamido ya musanta labarin da ya danganta shi da kujerar mataimakin Goodluck Jonathan a 2027.

Sule Lamido ya yi magana kan hada shi da Jonathan takara
Sule Lamido ya karyata cewa Obasanjo yana son ya zama mataimakin Jonathan. Hoto: Goodluck Jonathan, Olusegun Obasanjo.
Source: Twitter

Sule Lamido ya bayyana haka ne yayin hira da jaridar Daily Trust inda ya yi karin haske kan zaben 2027.

Kara karanta wannan

2027: Atiku ya ba da ƙafa, ya faɗi abin da ya sa yake takarar shugaban ƙasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2027: Lamido ya ba PDP shawara kan Jonathan

Wannan ya zo ne kwanaki bayan Lamido ya bayyana cewa Jonathan shi ne mafi dacewa da PDP domin tumbuke shugaba Tinubu da APC a 2027.

Ya bukaci PDP ta yi kokari wajen dawo da Jonathan cikin jam’iyya, yana mai cewa babu wani dan kudu da kwarewar da ya kai shi.

A wata hira da Channels TV, Lamido ya ce:

“Ina tunanin a yanzu jam'iyyar PDP ya kamata ta yi magana da Jonathan saboda shi ne kaɗai mafita gare su."

Ya bayyana Jonathan a matsayin shugaba da ya kware a mulki, kuma wanda ya taba shugabantar kasa tare da yin aiki da sauran shugabanni.

Sule ya ba PDP shawara kan takarar Jonathan
Sule Lamido ya ƙaryata yin takara da Jonathan. Hoto: Sule Lamido.
Source: Twitter

Sule Lamido ya magantu kan tsayawa da Jonathan

An jita-jita cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya zabe shi cikin shirin tumbuke Bola Tinubu da jam’iyyar APC a babban zaben gaba.

Kara karanta wannan

ADC: An samu wanda zai dawo da tallafin man fetur idan ya zama shugaban kasa a 2027

Lamido ya ce bai taba jin labarin daga Obasanjo kai tsaye ba, saboda haka bai dauki hakan da muhimmanci ba.

Ya ce yana shakku kan gaskiyar abubuwan da ake dorawa wa Obasanjo idan ba ya ji daga bakinsa kai tsaye ba, wannan batu kuma sabon abu ne a gare shi.

Sule Lamido ya bayyana cewa:

"Obasanjo tsohon shugaban kasa ne, kuma shugaba na a siyasa kuma zai ci gaba da kasancewa shugabana."

Ya ce idan lamarin gaskiya ne, da ya ji daga Obasanjo kai tsaye ba daga ’yan jarida ko kafafen watsa labarai ba inda ya shawarci a yi watsi da rahoton.

A wani bangare kuma, Sule Lamido ya bayyana cewa hadakar jam’iyyun adawa na 2027 na iya yin kuskure idan suka dauki dan takara mara karfi.

Sule Lamido ya shawarci PDP kan matsalolinta

Kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya nuna takaicinsa kan yadda wasu shafaffu da mai ke yin abin da suka ga dama a PDP

Sule Lamido ya yi kira da a hanzarta hukunta mutanen da suka yi fito na fito da jam'iyyar adawar lokacin zaben shekarar 2023.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa zai kauracewa tarurrukan kwamitin amintattun PDP har sai an ladabtar da irin wadannan mutanen.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.