A Karshe, INEC Ta Bayyana Sakamakon Zaben Cike Gurbin 'Dan Majalisa a Zamfara
- A ranar Alhamis, 21 ga watan Agusta, 2025, INEC ta karisa zaben mazabar dan majalisar dokokin Zamfara mai wakiltar Kaura Namoda ta Kudu
- Hakan ya biyo bayan ayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba sakamakon soke kuri'un wasu mazabu biyu a ranar Asabar
- Bayan tattara jimullar sakamako, jami'in INEC ya bayyana dan takarar APC a matsayin wanda ya samu nasara da kuri'u mafi rinjaye
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara - Dan takarar jam’iyyar APC, Kamilu Sa’idu, ya samu nasarar lashe zaɓen cike gurbi na mazabar Kaura Namoda ta Kudu a majalisar dokokin jihar Zamfara.
Lawal Sa’ad, jami’in tattara sakamako kuma Farfesa a Jami’ar Tarayya ta Gusau, ya bayyana sakamakon karshe da APC ta samu nasara a jiya Alhamis, 21 ga watan Agusta, 2025.

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta tattaro cewa INEC ta bayyana cewa APC ta lashe zaben da kuri’u 8,182, yayin da dan takarar jam’iyyar PDP, Muhammad Lawal Kurya, ya samu kuri'u 5,543.

Kara karanta wannan
INEC: 'Dan takara da ke daure a gidan yari ya lashe zaben dan majalisa a Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da ya faru a zaben majalisa a Zamfara
Zaben cike gurbi na dan Majalisar dokokin Zamfara mai wakiltar mazabar Kaura Namoda ta Kudu na daya daga cikin zabukan da INEC ta gudanar ranar Asabar, 16 ga watan Agusta, 2025.
Sai dai bayan kammala zaben, INEC ta ayyana shi a matsayin 'inconclisove' watau wanda bai kammalu ba sakamakom soke kuri'un mazabu biyu, Sakajiki sa Kyambarawa.
A jiya Alhamis, INEC ta karisa zaben a wadannan mazabu guda biyu, kuma bayan tattara sakamako, dan takarar APC ya samu nasara da kuri'u mafi rinjaye.
Hukumar INEC ta shirya wannan zaɓe a rumfunan zaɓe guda biyar da abin ya shafa, bayan dakatar da tattara sakamakon farko da aka yi ranar Asabar, rahoton Channels tv.
PDP ta nuna damuwa kan zaben Kaura Namoda
Amma tun kafin karisa zaben a jiya Alhamis, mai magana da yawun PDP na ƙasa, Debo Ologunagba, ya yi zargin cewa an tsoratar da masu jefa kuri’a a mazabar Kaura Namoda ta Kudu.
Ya kuma yi gargadin cewa jam’iyyar PDP, “Ba za ta amince da duk wani sakamako da bai yi daidai da ainihin ra’ayin jama’a ba."

Source: Facebook
APC ta samu nasara a zaben dan Majalisar Zamfara
Bayan karisa zaben kamar yadda doka ta tanada, jami'in INEC a mazabar, Lawal Sa'adu ya bayyana jimullar sakamakon cewa APC ta samu kuri'u 8,182 yayin da PDP ke da 5,543.
“Kamilu Sa’idu na jam’iyyar APC, wanda ya samu mafi yawan kuri’u, na ayyana shi a hukumance a matsayin wanda ya lashe zaɓen kuma ya zama zababben wakili,” in ji Sa’adu.
An gudanar da zabe a Kaura Namoda ta Kudu ne domin cike gurbin Aminu Ibrahim Kasuwar Daji, na jam’iyyar APC wanda ya rasu a ranar 9 ga watan Afrilu.
APC ta lashe zaben Ghari da Tsanyawa a Kano
A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar APC ta lashe zaben mazabar Ghari/Tsanyawa a jihar Kano, bayan ta lallasa abokiyar hamayyarta na NNPP.
Jami’in INEC a mazabar, Farfesa Muhammad Waziri na Jami’ar Bayero, ne ya bayyana sakamakon zaben bayan kammala tattara kuri'un da aka kada a zaben cike gurbin.
Ya bayyana cewa Garba Ya’u Gwarmai na jam’iyyar APC ya yi nasara da ƙuri’u 31,472.', inda ya doke Yusuf Ali Maigado na NNPP, wanda ya samu ƙuri’u 27,931.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
