Tunji Ojo: Minista Ya Cika Baki kan Tazarcen Shugaba Tinubu a 2027
- Ministan harkokin cikin gida, Olabunmi Tunji-Ojo, ya hango nasarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027
- Olabunmi Tunji-Ojo ya bayyana cewa tazarcen Shugaba Tinubu abu ne wanda ya tabbata, sai dai a jira lokaci kawai
- Ministan ya nuna cewa akwai 'yan Najeriya da dama wadanda suka shirya goyon bayan su saboda gamsuwa da kamun ludayin mulkinsa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan harkokin cikin gida, Hon. Olubunmi Tunji-Ojo, ya yi magana kan tazarcen shugaban kasa Bola Tinubu a 2027.
Olabunmi Tunji-Ojo ya bayyana cewa tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, abu ne wanda ya riga ya tabbata.

Source: Twitter
Tunji-Ojo ya ba da tabbacin ne a Abuja yayin da yake karɓar tawagar Grassroots Movement for Tinubu (GMT) karkashin jagorancin daraktanta, Hon. Bayowa Foresythe, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan
"Ka ajiye Shettima": An gayawa Tinubu wanda ya fi dacewa ya zama mataimakinsa a 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tawagar ta mika wasikar godiya daga shugaban kungiyar na kasa, Hon. Bisi Yusuf, ga ministan.
Me Tunji-Ojo ya ce kan tazarcen Tinubu?
Ministan ya jaddada kudurinsa na goyon bayan shirye-shiryen wayar da kan jama’a da kuma ayyukan da za su karfafa nasarorin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ya bayyana cewa tazarcen Shugaba Tinubu “ya riga ya tabbata”, yana mai danganta hakan da goyon bayan jama’a da shugaban ke ci gaba da samu a fadin kasar nan, musamman a jihar Ondo.
Tunji-Ojo ya tabbatar da cewa al’ummar Ondo za su ci gaba da tsayawa tsayin daka tare da Tinubu, rahoton The Punch ya tabbatar.
Ya yi alkawarin karfafa gangamin wayar da kan jama’a don tallafa wa manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Tinubu.
"Dole ne mu yi iyakar kokarinmu wajen tallafa wa shugaban kasa. Ba zan zauna a Abuja ba, na kasa mika tallafi ga jama’ata a Ondo, ko ta hanyar wayar da kan jama’a, ayyukan jam’iyya, ko shirye-shiryen da ke rage wa mutane wahala.”
"A karshe abin da ake magana akai shi ne kuri’u, kuma kowace kuri’a tana da muhimmanci. Shugaba Bola Tinubu zai lashe zaɓen 2027.”
- Olabunmi Tunji-Ojo

Source: Facebook
Minista ya ce Tinubu na da magoya baya
Haka kuma ya jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin gwamnati, jam’iyya da kungiyoyin masoya masu zaman kansu wajen karfafa goyon baya ga gwamnatin Shugaba Tinubu.
"Akwai ’yan Najeriya wadanda saboda gamsuwa, suke son su goyi bayan shugaban kasa ba tare da dole sai sun bi jam’iyya ba."
- Olabunmi Tunji-Ojo
Kungiyar NENF ta ba Tinubu shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar NENF ta ba da shawara ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, kan wanda ya dace ya yi masa mataimaki a zaben 2027.
Kungiyar NENF ta bukaci Shugaba Tinubu ya ajiye Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa, sannan ya dauko Kirista a matsayin abokin takararsa a zaben 2027.
Ta bayyana cewa tikitin Muslim/Muslim ya yi wa jam'iyyar APC illa a zaben 2023, kuma tarihi zai maimaita kansa a 2027, idan Tinubu bai sauya mataimaki ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
