'Dalilin da Ya Sa Ya Kamata Jonathan Ya Jagoranci Najeriya a 2027'

'Dalilin da Ya Sa Ya Kamata Jonathan Ya Jagoranci Najeriya a 2027'

  • Ana ci gaba da yin kira ga Goodluck Jonathan kan ya nemi takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027 da ake tunkara
  • Tsohon dan takarar shugaban kasa, Mathias Tsado, ya bukaci makusantan Jonathan da su lallaba shi ya sake jaraba sa'arsa a 2027
  • Mathias Tsado ya bayyana cewa ana bukatar Jonathan ya sake tsayawa takara domin ya farfado da kasar nan daga halin da take ciki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Mathias Tsado, ya ba da shawara ga makusantan Goodluck Jonathan.

Mathias Tsado ya bukaci makusantan Jonathan da su lallashe shi ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027.

An bukaci Jonathan ya tsaya takarar shugaban kasa
Shugaban kasa Bola Tinubu da Goodluck Jonathan a wajen wani taro Hoto: @DOlusegun, @GEJonathan
Source: Twitter

Mathias Tsado ya yi wannan kira ne a wata hira da aka yi da shi a shirin 'Sunrise Daily' na tashar Channels tv a ranar Talata, 19 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan

2027: Shehu Sani ya ba Goodluck Jonathan shawara kan shiga takarar shugaban kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bukaci Jonathan ya nemi shugabancin Najeriya

Ya ce dawowar Jonathan kan mulki ita ce mafita mafi dacewa wajen magance matsalolin tattalin arziki da tsaro da ke kara ta’azzara a Najeriya.

"Muna bukatarsa ya dawo a 2027. Wannan ba batun siyasa ba ne, batun ceto Najeriya ne. Yana da kwarewa, halayya da hangen nesa da za su iya farfado da kasarmu daga halin da take ciki."

- Mathias Tsado

A cewarsa, mulkin Jonathan ya bar kyakkyawan tarihi wajen bin ka’idojin dimokuraɗiyya da sauye-sauye da za a iya farfaɗowa da su domin dawo da daidaito a kasar nan.

Ya kara da cewa har yanzu mutane da dama a Najeriya suna kallon tsohon shugaban kasan a matsayin mutum mai haɗa kan jama’a.

Ana son makusantan Jonathan su lallashe shi

Mathias Tsado ya kuma yi kira ga abokan siyasar Jonathan da su kara kaimi wajen rarrashinsa, yana mai jaddada cewa kasar nan tana cikin mawuyacin hali.

Kara karanta wannan

Ana zargin sukar gwamnati ta jawo kai hari kan jigon APC, ya sha da ƙyar a Abuja

"Wadanda ke kusa da shi su haɗa baki su yi magana da shi da murya ɗaya. Najeriya na buƙatarsa fiye da baya."
"Salon shugabancinsa ne kaɗai zai iya kwantar da hankali da kuma mayar da tattalin arziƙi kan turbar da ta dace."

- Mathias Tsado

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan
Hoton tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a wajen wani taro Hoto: Goodluck Jonathan
Source: Facebook

Wannan kira na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin siyasa game da wadanda ake ganin akwai yiwuwar za su tsaya takara a zaben shugaban ƙasa na 2027.

Duk da cewa Jonathan bai nuna shawa'ar tsayawa takara ba, Mathias Tsado ya dage cewa tsohon shugaban kasan har yanzu shi ne babban wanda zai iya dawo da kasar nan kan turbar da ta dace.

Shehu Sani ya shawarci Jonathan

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Shehu Sani, ya shawarci tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, kan yin takara a zaben 2027.

Sanata Shehu Sani ya shwarci Jonathan kan ka da ya ba ta lokacinsa wajen yin takarar shugaban kasa.

Tsohon sanatan na Kaduna ta Tsakiya, ya bayyana cewa jam'iyyar PDP da Jonathan ya sani baya, a yanzu ba ita ba ce domin abubuwa sun tabarbare a cikinta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng