"Da Bakinsu Suka Fada," Buba Ya Gano Abin da Gwamnatin Tinubu Ta Shirya Yi a Zaben 2027
- Buba Galadima ya zargi gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu da shirin murde zaben 2027
- Jigon jam'iyyar NNPP ya bayyana cewa sun shirya tsaf domin koya wa wannan gwamnati ta APC darasi a zabe mai zuwa
- Ya kuma yi fatali da zaben cike gurbin da INEC ta gudanar a karshen makon jiya, a cewarsa an saba wa kundin dokokin zabe
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Buba Galadima, babban jigo a NNPP kuma daya daga cikin na hannun daman jagora, Rabiu Kwankwaso ya ce sun gano yadda ake shirya murde zabe.
Buba ya zargi gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da shirin yin maguɗin zaɓe a shekarar 2027.

Source: Twitter
Jigon na NNPP ya bayyana haka ne a shirin ‘Politics Today’ na tashar Channels tv a ranar Litinin, 18 ga watan Agusta, 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Buba Galadima ya zargi gwamnatin Tinubu da magudi
Ya ce jam’iyyarsu ta NNPP za ta koyawa gwamnati mai ci darasi a babban zaɓen da ke tafe.
“Abin da ke gudana a yanzu abu ne mai sauƙi, shirin wannan gwamnati shi ne yin maguɗin zaɓe a 2027," in ji shi.
Da aka tambaye shi yadda ya san wannan shirin murdiya a zaben 2027, Buba Galadima ya ce:
“Daga halayensu, sun fito sun faɗa a fili. Idan suka je wurin wani gwamna, suna kafa sharadi, ya sauya sheka ko su kwace mulki daga gare shi ba ta hanyar kada kuri'a ba. Abin da suke yi kenan.
Jigon NNPP na zargin an lalata siyasar Najeriya
Ya kara da cewa ba a sukar gwamnatin Tinubu yadda ya kamata saboda yan siyasa masu gaskiya da rikon amana sun yi karanci a kasar nan.
Buba Galadima ya ce siyasar Najeriya ta gurbace domin cike take da masu neman dama kawai, ba masu kishin kasa da talakawa ba, cewar rahoton Vanguard

Kara karanta wannan
Malamin addini ya yi hasashe kan tazarcen Tinubu, ya fadi sharadin da zai sa ya sha kaye
Ya ce duk gwagwarmayar da ya yi a tsawon lokacin da ya shafe a siyasa, ba a taba zabensa a wani mukami ba saboda ana kallonsa a matsayin “mara kyau” a siyasar Najeriya.

Source: Facebook
'Hukumar INEC ta karya dokar zaben cike gurbi'
Game da zaɓen cike gurbi da aka kammala a cikin jihohi 13 a karshen mako, Buba Galadima ya zargi INEC da jagorantar abin da ya kira da “karya doka.”
"Maganar gaskiya gaba daya wannan zaben cike girbin da aka yi, INEC ta gudanar da su ba bisa ka'ida ba.
"Idan aka samu kujerar da babu kowa, ya zama wajibi bisa tanadin doka, INEC ta cike wannan gurbi cikin watanni uku, amma wasu daga cikin mazabun da aka yi zaben sun kai shekara biyu babu kowa."
- Buba Galadima.
Wani jigon NNPP, Abdullahi Sa'idu ya fadawa Legit Hausa cewa sun fara shirye-shiryen tunkarar zaben 2027, kuma babban abin da suka sa a gaba shi ne nasarar Kwankwaso.
A cewarsa, babu wani dan takara da suke tsoro domin kowa ya san nagartar jagoran NNPP.
"Maganar gaskiya babu alamar wannan gwamnatin za ta bari a kayar da ita, amma ba za mu ji tsoro ba, mulki na Allah ne, kuma shi ke bai wa wanda ya so.

Kara karanta wannan
"Ka ajiye Shettima": An gayawa Tinubu wanda ya fi dacewa ya zama mataimakinsa a 2027
"Mu fatanmu shi ne Najeriya ta gyaru, 'yan Najeriya suna ganin abin da ke faruwa kuma su za su yanke hukunci a babban zabe mai zuwa," in ji shi.
Kwankwaso zai hada kai da Tinubu kafin 2027?
A wani labarin, kun ji cewa Buba Galadima ya bayyana cewa watakila Rabiu Kwankwaso ba zai hada kai da Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027 ba.
Ya ce gwamnatin Tinubu ta yi wa Kwankwaso da NNPP rashin adalci a Kano ta hanyar goyon bayan tsohon Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero duk da an tsige shi.
Buba wanda ke da kusanci da Kwankwaso a siyasa, ya yi ikirari cewa jam'iyyar NNPP ce za ta yanke wanda zai zama shugaban Najeriya a 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
