'Abin da Ya Sa APC Ta Lashe Mafi Yawan Zabukan Cike Gurbi da Aka Yi a Kano da Jihohi 12'
- Jam'iyyar APC ta samu nasara a mafi yawan mazabun da aka gudanar da zaben cike gurbi a jihohi 13 a Najeriya a karshen makon jiya
- APC reshen jihar Legas ta ce jama'a sun fito sun zabi jam'iyyar ne saboda su kara nuna gamsuwa da goyon bayan gwamnatin Bola Tinubu
- Mai magana da yawun APC a Legas ya ce nasarorin da APC ta samu ranar Asabar karkashin shugabancin Nentawe Yilwatda sun shiga tarihi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - An bayyana zabukan cike gurbi da aka gudanar ranar Asabar a mazabu 16 na tarayya da na jihohi a matsayin raba gardama kan mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
APC reshen jihar Legas ce ta bayyana hakan, tana mai cewa nasarar da jam'iyyar ta samu a fadin jihohi 13 ya nuna cewa har yanzu 'yan Najeriya na kaunar jam'iyya mai mulki.

Asali: Twitter
Daily Trust ta tattaro cewa sakamakon zabukan da aka gudanar a ranar Asabar, 16 ga watan Agusta, 2025 ya nuna APC ta yi nasara a kujeru 12 daga cikin 16 da aka yi a Kano da wasu jihohi 12.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC: 'Yan Najeriya na tare da Tinubu
Mai magana da yawun APC a Legas, Seye Oladejo, a cikin wata sanarwa ya ce nasarar da jam'iyyar ta samu ya tabbatar da cewa ita ke da rinjayen magoya baya a Najeriya.
A cewarsa, masu kada kuri’a sun nuna gamsuwa da shugabancin Shugaba Tinubu da sabuwar tafiyar jam’iyyar APC a ƙarƙashin jagorancin Farfesa Nentawe Yilwatda.
"Wannan zagayen zaben cike gurbi shi ne na farko tun bayan da Farfesa Yilwatda ya karɓi ragamar shugabancin APC, kuma nasarar da aka samu ta shiga tarihi.
“Daga Arewa zuwa Kudu, jama’a sun yi magana da babbar murya ta hanyar akwatun kuri’a.
"Nasarorin APC, ciki har da kujerar Sanatan Edo ta Tsakiya, kujerun majalisar wakilai a Kaduna, Jigawa, Ogun da Edo, da kujerun majalisar jiha a Adamawa, Taraba, Neja, Ekiti da Kano, sun nuna godiyar jama’a ga manufofi, gyare-gyare da salon mulkin gwamnatin Tinubu.”

Kara karanta wannan
PDP ta yi kuka da zaɓe a Zamfara, ta yi zargin sojoji da ƴan ta'adda sun jawo matsala
- In ji Seye Oladejo.
APC reshen Legas ta kara da cewa duk da yadda ‘yan adawa suka yi ta yada farfaganda da ƙalubalen tattalin arziki, gwamnatin Tinubu ta nuna jajircewa kan manufofinta.

Asali: Getty Images
Me yasa APC ta samu nasarori a zabukan?
APC ta ce duk da matsin lamba, gwamnatin ta mai da hankali wajen daidaita tattalin arziki, yaki da rashin tsaro, habaka gine-ginen more rayuwa da kuma ɗaukar matakan gyaran tsarin musayar kudi, rahoton Vanguard.
"Ba komai ya sa APC ta samu wannan masara ba face amincewar da yan Najeriya suka yi da tsare-tsaren gwamnatin Tinubu,"
"Masu kada kuri'a sun raba gardama, sun nuna cewa sun gamsu kuma suna tare da gwamnatin Tinubu musamman a jihohin Kaduna, Adamawa, Taraba da Edo," in ji Oladejo.
Tinubu ya taya wadanda suka yi nasara murna
A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya taya waɗanda suka lashe zaɓukan cike gurbi da aka gudanar ranar Asabar murna.
Shugaban Bola Tinubu ya yaba wa hukumar INEC bisa yadda ta shirya kuma ta gudanar da zaɓukan lafiya ba tare da wata tangarda ba.
Haka zalika, ya jinjinawa sabon shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, saboda jagorantar jam’iyyar zuwa wannan babbar nasara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng