Zabukan Cike Gurbi: Tinubu Ya Yaba da Nasarar APC, Ya Aika Sako ga INEC

Zabukan Cike Gurbi: Tinubu Ya Yaba da Nasarar APC, Ya Aika Sako ga INEC

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan zabukan cike gurbi da hukumar zabe ta INEC ta gudanar a wasu mazabun kasar nan
  • Mai girma Bola Tinubu ya taya 'yan takarar da suka samu nasara murna a zaben wanda aka gudanar a mazabu 16 da ke cikim jihohi
  • Hakazalika, ya yabawa hukumar INEC kan yadda ta gudanar da zaben cikin lumana ba tare da tashin hankali ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya murna ga waɗanda suka lashe zaɓukan cike gurbi da aka gudanar ranar Asabar, 16 ga watan Agusta, a mazabu 16 da ke jihohi 12.

A zabukan da aka gudanar dai, jam’iyyar APC ta samu nasara a mazabu 12 na jihohin da aka gudanar.

Tinubu ya yi magana kan zabukan cike gurbi
Hoton Shugaba Bola Tinubu a wajen wani taro Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labaru da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin Lahadi a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro ya faɗi a mazaɓarsa kamar yadda ake yaɗawa? Badaru ya magantu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta samu nasara a zabukan cike gurbi

Da yake bayyana sakamakon zaɓen, Onanuga ya ce APC ta yi nasara a mazabu 12, jam’iyyar APGA ta samu nasara a mazabu biyu, PDP ta yi nasara a mazaba daya, yayin da NNPP ta lashe zabe a mazaba daya.

Sanarwar ta bayyana cewa shugaban kasa ya yaba wa INEC saboda gudanar da zaɓukan lafiya ba tare da wata tangarda ba, galibin su kuma ba tare da tashin hankali ba.

Haka kuma ya jinjinawa sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, saboda jagorantar jam’iyyar zuwa wannan babbar nasara ta farko a karkashin shugabancinsa.

Shugaba Tinubu ya kuma taya gwamnonin APC da sauran shugabanni murna bisa nasarar da aka samu a zaɓukan cike gurbin.

Tinubu ya yabawa shugaban APC

“Shugaba Nentawe Yilwatda ya nuna ƙarfin jagoranci kuma ya tabbatar da abin da za a iya cimmawa idan aka tsayar da ‘yan takara da jama’a ke so tare da haɗin kai tsakanin shugabannin jam’iyya.”

Kara karanta wannan

Nasarar APC, PDP, NNPP: INEC ta bayyana sakamakon zabukan cike gurbi a jihohi 8

"Ga dukkan mambobin APC da masu zaɓe, na gode saboda amincewar da kuka ba jam’iyyarmu."
"Muna baku tabbacin cewa takenmu na Renewed Hope ba na banza ba ne. Burinmu shi ne samun Najeriya mafi kyau, mafi tsaro mai yalwar arziki. Da ikon Allah, za mu kai ku can."

- Shugaba Bola Tinubu

Tinubu ya tabo batun zaben cike gurbi
Shugaba Bola Tinubu yayin wani jawabi ga 'yan Najeriya Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Shugaban ƙasa Tinubu ya kuma yaba wa dukkan jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da suka shiga zaɓukan.

APC ta lashe zabe a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da sakamakon zaben Ghari/Tsanyawa na majalisar dokokin jihar Kano

Dan takarar jam'iyyar APC, Ya'u Garba Gwarmai, ya lallasa abokin hamayyarsa na NNPP, Yusuf Ali Maigado.

Ya'u Garba Gwarmai ya lashe zaben ne bayan ya samu kuri'u 31,472, yayin da Yusuf Ali Maigado na jam'iyyar NNPP wanda ya zo na biyu a zaben, ya samu kuri'u 27,931.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng