Nasarar APC, PDP, NNPP: INEC Ta Bayyana Sakamakon Zabukan Cike Gurbi a jihohi 8

Nasarar APC, PDP, NNPP: INEC Ta Bayyana Sakamakon Zabukan Cike Gurbi a jihohi 8

Hukumar INEC ta fitar da sakamakon zabukan cike gurbi da aka gudanar a jihohi daban–daban a Najeriya, a ranar Asabar, 16 ga Agusta, 2025.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Manyan jam’iyyun siyasa — APC, PDP, NNPP, da APGA — da suka fafata a zabukan, sun samu nasarori a mazabun jihohi daban-daban.

Hukumar INEC ta bayyana sakamakon zabukan cike gurbi da ta gudanar a wasu jihohin Najeriya.
Jami'an hukumar INEC suna tattara sakamakon zaben da aka kada a jihar Edo a 2024. Hoto: Imranmuhdz/X
Asali: Getty Images

Rahoton NTA News ya nuna cewa INEC ta gudanar da zabukan ne domin cike gurbin kujerun da suka zama babu mai rike da su a majalisar tarayya da kuma majalisun dokokin jihohi.

Yayin da APC ta tabbatar da rinjayenta a wasu mazau, PDP da APGA ma sun nuna karfi a nasu mazabun, inda NNPP kuma ta ci gaba da kafa tarihi a jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da cewa, an gudanar da zabukan cikin kwanciyar hankali a mafi yawan jihohi, hukumar INEC ta bayyana daya daga cikin zabukan a matsayin wanda bai kammalu ba saboda wasu matsaloli.

Kara karanta wannan

Zabukan cike gurbi: Tinubu ya yaba da nasarar APC, ya aika sako ga INEC

Cikakken bayani kan sakamakon zabukan

1. Jihar Kogi

Jami'in tattara zaben cike gurbi na mazabar Okura-II, Farfesa Emmanuel Eneche, ya bayyana Musa Hassan Yakubu na APC a matsayin wanda ya yi nasara da kuri’u 55,073.

2. Jihar Neja

A mazabar Munya, Mathew Dogara Daje na APC ya samu kuri’u 12,733, inda ya doke Sabo Sunday Adabyinlo na PDP wanda ya samu kuri’u 5,907, a cewar kwamishinan INEC na jihar, Ahmed Yusha’u Garki.

3. Jihar Anambra

Dr Emmanuel Nwachukwu na jam'iyyar APGA ne ya lashe zaben Sanatan Anambra ta Kudu da kuri’u 9,640.

A hannu daya kuma, hukumar INEC ta ce Mimi Azikiwe ta jam'iyyar APGA ta yi nasara a zaben mazabar Onitsha ta Arewa 1 da kuri’u 7,774.

4. Jihar Zamfara

INEC ta bayyana zaben majalisar jihar na Kaura-Namoda ta Kudu a matsayin wanda bai kammalu ba, a cewar jami'in tattara sakamakon zaben (R.O), Farfesa Lawal Sa’ad.

Kara karanta wannan

Hukumar INEC ta ce akwai kura a zaben Zamfara, ta ayyana shi 'inconclusive'

5. Jihar Jigawa

A mazabar Babura/Garki ta tarayya, Muktar Rabiu Garki na jam'iyyar APC ya yi nasara da kuri’u 38,449, inda PDP ta samu 13,519.

Hukumar INEC ta fadi sakamakon zabukan cike gurbi da aka yi a wasu jihohin Najeriya
Jami'an INEC na tattara sakamakon zabe yayin da jami'an tsaro da na jam'iyyu ke sanya ido. Hoto: @Imranmuhdz/X
Asali: Twitter

6. Jihar Kano

A zaben Ghari/Tsanyawa, Garba Ya’u Gwarmai na APC ya samu kuri’u 31,472, inda ya doke dan takarar NNPP da kuri’u 27,932, kamar yadda Farfesa Muhammad Waziri ya bayyana.

NNPP ta lashe zabe a Bagwai/Shanono inda dan takararta Ali Hassan Kiyawa ya samu kuri’u 16,198, yayin da dan takarar APC, Ahmad Muhammad Kadamu ya samu 5,34.

7. Jihar Ogun

INEC ta bayyana Adesola Ayoola Elegbeji ta APC a matsayin wadda ta lashe kujerar mazabar Remo a majalisar tarayya, kamar yadda muka ruwaito.

8. Jihar Oyo

INEC ta bayyana Folajimi Oyekunle na PDP a matsayin wanda ya lashe kujerar majalisar wakilai ta Ibadan North da kuri’u 18,404, inda dan takarar APC ya samu 8,312.

An kama jami'an INEC 3 a Taraba

Kara karanta wannan

APC, PDP sun sha kashi a zaben cike gurbin Sanata Ubah da ya rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ƴan sanda a Taraba sun kama jami’an INEC uku da suka karkatar da kayan zaɓe a mazabar Karim Lamido I.

An kwato akwatin jefa kuri’u uku, na’urorin BIVAS biyu, takardun kuri’u 20, takardun rubuta sakamakon zaɓe biyu da sauransu.

Kafin zaɓen, APC ta kafa kwamitin yaƙin neman zaɓe na mutum 60 ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.