Tirkashi: 'Yan Sanda Sun Cafke Jami'an INEC 3, An Kwato Kayayyakin Zabe a Taraba
- Rundunar ƴan sanda a Taraba ta kama jami’an INEC uku da suka karkatar da kayan zaɓe zuwa wani gida a mazabar Karim Lamido I
- An kwato akwatin jefa kuri’u uku, na’urorin BIVAS biyu, takardun kuri’u 20, takardun rubuta sakamakon zaɓe biyu da sauransu
- Kafin zaɓen, APC ta kafa kwamitin yaƙin neman zaɓe na mutum 60 ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Taraba - Rundunar ƴan sanda a jihar Taraba ta cafke wasu jami’an hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) tare da kwato kayayyakin zaɓe.
Ana zargin jami'an INEC din da karkatar kayayyakin zaben yayin zaɓen cike gurbi na mazabar Karim Lamido I a majalisar dokokin jihar.

Source: Twitter
'Yan sanda sun kama jami'an INEC 3
Majiyar Zagazola Makama ta tabbatar a ranar Lahadi cewa 'yan sanda sun cafke jami'an INEC da kwato kayayyakin ne bayan sahihin bayanai da wakilan jam’iyyu suka bayar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 16 ga Agusta, misalin ƙarfe 2:20 na rana, lokacin da tawagar ƴan sanda ta kama waɗanda ake zargi a wani gida dake kauyen Angwan Sarkin Panya.
Wadanda aka cafke sun haɗa da Gideon Amos, wanda aka tura a matsayin jami'in INEC a rumfar zaɓe ta PU 16, Angwan Yusuf Dogo, Bikwin Ward, da kuma wasu jami'ai biyu: Matthew Jayi, da Tiasama Mathias Musa.
Ana zargin jami'an INEC din uku da karkatar da kayan da aka tanada domin rumfunan zaɓe uku — PU 005 Gandara, PU 016 Angwan Yusuf Dogo, da PU 029 da ke cikin makarantar firamare ta Angwan Sarki — zuwa gidan da aka kama su.
'Yan daba sun kwace kayan jami'in 'yan sanda
Kayan da aka kwato daga hannunsu sun haɗa da akwatin jefa kuri’u uku, na’urorin BIVAS biyu, jadawalin masu kada kuri’a 19, takardun kuri’a 20, tamɓarin INEC biyu tare da tawada, alƙalami ɗaya da kuma takardun sakamakon zaɓe biyu.
Majiyar ta ƙara da cewa a lokacin da ake ƙoƙarin hana karkatar da kayan, 'yan daba sun yi wa wani ɗan sanda mai suna PC Christian Garba da yake bakin aiki fashi, inda suka kwace kakinsa kuma tsere da kayan.
Haka kuma an rahoto cewa an kammala kada kuri'a a yawancin rumfunan zaɓen mazabar, inda aka shiga matakin tattara sakamakon, yayin da ake bincike kan wadanda aka kama.

Source: Twitter
Taraba: APC ta kafa kwamitin mutum 60
Kafin zaɓen, jaridar The Guardian ta ruwaito cewa jam’iyyar APC ta naɗa tsohon gwamnan Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, a matsayin shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓe na mazabar Karim 1, jihar Taraba.
Haka zalika, an naɗa Hajiya Imam Sulaoman-Ibrahim, Sanata Sani Musa, Orji Uzor Kalu, Kaka Shehu da Jim Kuta a matsayin mataimakan shugabanni, yayin da Farfesa Suwaiba Saidu Ahmad za ta kasance sakatariyar kwamitin.
Waɗannan sun haɗu da mambobi 60 na kwamitin yaƙin neman zaɓen da aka tura domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a wannan zabe na cike gurbi.
NNPP, APC sun lashe zabuka a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jam’iyyar NNPP da kuma APC sun lashe zabukan cike gurbi daban–daban na majalisar dokokin jihar Kano.
NNPP ta lashe zabe a Bagwai/Shanono inda dan takararta Ali Hassan Kiyawa ya samu kuri’u 16,198, yayin da na APC ya samu 5,347.
A mazabar Ghari/Tsanyawa, INEC ta ce dan takarar APC Garba Ya’u Gwarmai ya samu kuri’u 31,472, inda ya doke NNPP mai kuri'u 27,931.
Asali: Legit.ng


