Hukumar INEC Ta Ce Akwai Kura a Zaben Zamfara, Ya Ayyana Shi ‘Inconclusive’

Hukumar INEC Ta Ce Akwai Kura a Zaben Zamfara, Ya Ayyana Shi ‘Inconclusive’

  • INEC ta bayyana zaben majalisar dokoki a Kaura Namoda ta Kudu, Zamfara, a matsayin wanda bai kammalu ba
  • APC ta samu kuri’u 7,001, PDP ta samu 5,339, bambancin bai kai yawan masu katin zabe na wuraren da aka soke ba
  • INEC za ta shirya zaben karin haske a rumfunan da abin ya shafa a Sakajiki da Kambarawa kafin a bayyana wanda ya yi nasara

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa zaben kujerar majalisar dokoki na Kaura Namoda ta Kudu a jihar Zamfara bai kammalu ba.

Wannan sanarwar ta fito daga bakin Farfesa Lawal Sa’adu, wanda shi ne jami’in tattara sakamakon zaben a jihar.

An ayyana zaben cike gurbi a Zamfara wanda bai kammalu ba
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma a Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

An soke wasu rumfunan zabe a Zamfara

Kara karanta wannan

APC, PDP sun sha kashi a zaben cike gurbin Sanata Ubah da ya rasu

Farfoesa Sa’adu ya bayyana cewa dalilin da ya sa aka dauki wannan mataki shi ne saboda soke sakamakon wasu rumfunan zabe a yankunan Sakajiki da Kambarawa, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, yawan masu rijista a wuraren da aka soke ya kai 5,446, yayin da aka karbi katin zabe 3,265.

A cikin sakamakon da aka tattara, jam’iyyar APC ta samu kuri’u 7,001, yayin da jam’iyyar PDP ta samu kuri’u 5,339.

Musabbabin soke zaben cike gurbi a Zamfara

Bambancin kuri’u tsakanin su ya kasance 1,662 kacal, wannan bambanci bai kai yawan katin zaben da aka riga aka karba a wuraren da aka soke sakamakon ba.

Sa’adu ya yi nuni da cewa bisa ga dokar zabe ta shekarar 2022, idan irin wannan yanayi ya faru, dole ne a kira sabon zabe.

Hakan ya faru ne saboda ba za a iya bayyana wanda ya yi nasara ba har sai an kammala sake zaben.

Ya ce yankunan da abin ya shafa sun hada da Sakajiki, inda rumfunan zabe biyu ke da masu rijista 1,357 da kuma katin da aka karba 1,298.

Kara karanta wannan

Bayani dalla dalla: Yadda NNPP da APC suka lashe zabukan cike gurbi a jihar Kano

Zaben cike gurbi ta yi zafi a jihar Zamfara
Gwaman Dauda Lawal na ci gaba da takun-saka da Minista Bello Matawalle. Hoto: DaudanLawal, Dr. Bello Matawalle.
Source: Twitter

Yaushe za a sake gudanar da zabe a Zamfara?

Haka kuma, a Kambarawa akwai rumfunan zabe guda uku da ke da masu rijista 4,088 da kuma katin zabe 1,964 da aka karba.

A karshe, jami’in tattara sakamakon ya bayyana cewa hukumar zabe za ta sanar da sabon lokaci domin gudanar da karin zaben cike gurbi a rumfunan da abin ya shafa.

Wannan zai bai wa hukumar damar tabbatar da ingantaccen sakamako da gaskiya a cikin zaben, rahoton TheCable ya tabbatar.

APC ta lashe zaben cike gurbi a Chikun-Kajuru

Mun ba ku labarin cewa a jihar Kaduna, ɗan takarar APC Felix Joseph Bagudu ya lashe zaben cike gurbi na mazabar Chikun–Kajuru da kuri’u 34,580.

Farfesa Abubakar Jumare na INEC ya bayyana sakamakon, inda ya ce Bagudu ya doke PDP wacce ta samu kuri’u 11,491.

Sakamakon ya ƙara tabbatar da rinjayen APC a Kaduna, yayin da jam’iyyar hadakar 'yan adawa ta ADC ta samu kuri'u 3,477 .

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.