Bayani Dalla Dalla: Yadda NNPP da APC Suka Lashe Zabukan Cike Gurbi a Jihar Kano
- Jam’iyyar NNPP da kuma APC sun lashe zabukan cike gurbi daban–daban na majalisar dokokin jihar Kano da aka gudanar
- NNPP ta lashe zabe a Bagwai/Shanono inda dan takararta Ali Hassan Kiyawa ya samu kuri’u 16,198, yayin da na APC ya samu 5,347
- A mazabar Ghari/Tsanyawa, dan takarar APC Garba Ya’u Gwarmai ya samu kuri’u 31,472, inda ya doke NNPP mai kuri'u 27,931
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Jam’iyyar NNPP da kuma APC sun lashe zabukan cike gurbi daban–daban na majalisar dokokin jihar Kano da aka gudanar a ranar Asabar.
Wadannan nasarorin sun sake jaddada yadda ake tataburza tsakanin NNPP da APC wajen neman rinjaye a majalisar dokokin jihar Kano.

Asali: Twitter
NNPP ta lashe zaben Bagwai/Shanono
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa NNPP ta lashe kujerar majalisar jihar ta Bagwai/Shanono, inda aka gudanar da zaben cike gurbi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hassan Adamu Shitu, jami’in tattara sakamakon, ya sanar da sakamakon misalin ƙarfe 12:36 na safiyar ranar Lahadi, 17 ga Agusta, 2025.
Shitu ya bayyana cewa Ali Hassan Kiyawa na NNPP ya samu 16,198 inda ya doke Ahmad Muhammad Kadamu na APC wanda ya samu kuri’u 5,347 kacal.
An gudanar da zaben cike gurbin ne sakamakon mutuwar tsohon dan majalisar da ke wakiltar mazabar, Halilu Ibrahim Kundila na APC a watan Afrilu, 2024.
APC ta lashe zaben Ghari/Tsanyawa
Haka zalika, jam’iyyar APC ta lashe kujerar Ghari/Tsanyawa a zaben mazabar da aka sake gudanarwa a jihar Kano, kamar yadda rahoton Legit Hausa ya nuna.
Jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Muhammad Waziri daga jami’ar Bayero, ya ayyana Garba Ya’u Gwarmai na APC a matsayin zakara bayan ya samu kuri’u 31,472.
Ya doke dan takarar NNPP, Yusuf Ali Maigado, wanda ya samu kuri’u 27,931, a zaben da aka gudanar bayan an ce na farko bai kammalu ba.

Kara karanta wannan
Duk da tasirin El Rufai, APC ta lashe zaben cike gurbi da tazara mai yawa a Kaduna
APC ta nemi a soke zabukan jihar
Wannan na zuwa ne yayin da a ranar Asabar, APC ta bukaci INEC da ta soke zabukan jihar, tana zargin cewa an gurɓata su da tashin hankali da kuma tarzoma.
Felix Morka, kakakin APC na ƙasa, ya ce an samu “tashe-tashen hankula da hare-haren ‘yan daba masu dauke da makamai” a rumfunan kada kuri’a da dama.
Ya kuma ce rahotanni daga Shanono, Bagwai da Ghari sun nuna cewa masu kada kuri’a sun tsere daga rumfunan, yayin da jami’an tsaro ke ƙoƙarin shawo kan lamarin.

Asali: Original
NNPP ta yi tur da bukatar APC
Haka kuma, kwamishinan INEC na jihar Kano, Audu Zango, ya ce an kama sama da mutum 100 da ake zargin ‘yan daba ne a yayin zaben Bagwai, inji rahoton The Cable.
Sai dai kakakin NNPP, Ladipo Johnson, ya yi watsi da kiran soke zaben, yana mai cewa bukatar APC “ba ta da tushe kuma ba ta da wani hujja.”

Kara karanta wannan
Jam'iyyar APC ta lallasa PDP a zaben cike gurbi na dan majalisar Jigawa da ya rasu
Ya dage cewa an yi zabukan cikin kwanciyar hankali, gaskiya, ba tare da wani laifi na zabe ba, inda ya ƙara da cewa NNPP ba za ta shiga hurumin INEC a zaben ba duk da ita ke mulki a jihar.
Kaduna: APC ta lashe zabe a Chikun/Kajuru
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ɗan takarar APC Felix Joseph Bagudu ya lashe zaben cike gurbi na mazabar Chikun–Kajuru da kuri’u 34,580.
Farfesa Abubakar Jumare na hukumar INEC ya bayyana sakamakon, inda ya ce Bagudu ya doke PDP wacce ta samu kuri’u 11,491.
Sakamakon ya ƙara tabbatar da rinjayen jam'iyyar APC a Kaduna, yayin da jam’iyyar hadakar 'yan adawa ta ADC ta samu kuri'u 3,477 kacal.
Asali: Legit.ng